Posts

Kamfanin Dangote zai cigaba da karfafa dankon zumunci a tsakaninsa da al ummomi dake kewaye dashi.

Image
Kamfanin Dangote ya kara jaddada a niyyar shi na na ci gaba da zaman lafiya da al'ummomi dake kewaye da shi. Babban Manajan kamfanin, Malam Bello Danmusa ne ya baiynana haka yayin zaman ganawa da masu ruwa da tsaki da ya wakana a garin Numan. Babban Manajan kamfanin, Malam Bello Danmusa yace gina kyakkyawan alaka da al'umomi dake kewaye da kamfanin abu ne wanda ya dauka da muhimmanci matuka shi yasa ma ta shirya wannan taron ganawar. Danmusa yace, kamfanin Dangote dake Numan na aiki tare da al'umomin dake kewaye da shi a fannonin ilimi da aiyukan tallafi ta hanyoyi daya tsara domin inganta rayuwan mutanen da ke yankin. A cewar shi, kamfanin Dangote zai ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsakin domin yin hakan zai basu daman tattaunawa tare da bullo da hanyoyi da za a amfana, a kuma samu zaman lafiya tsakanin juna domin ci gaban kamfanin, al'ummomin, jaha dama kasa baki daya. Da yayi jawabi kan muhimmancin wannan zama, Babban Jami'in Ofishin hulda da al'u...

An taya gwamna. Fintir murna.

Image
Alhaji Suleiman Yusuf Jami in tsare tsaren aikin hajji karamar hukumar Madagali a jahar Adamawa ya taya gwamna Ahmadu Umaru Finti murnan rantsar dashi a matsayin gwamna karo na biyu a jahar Adamawa. Akhaji Yusuf yace yayi farincikin ganin an kammal bikin rantsar da gwamnan lafiya ba tare da watamatsalaba kuma ya na mai fatan gwamnan zaicigaba da gudanar da aiyukan cigaban jahar dama inganta tsaro a fadin jahar baki daya. Ya kuma kirayi daukacin al ummar jahar ta Adamawa da sukasance masu baiwa gwamnan hadin kai da goyon baya domin ganin gwamnan ya samu damar gudanar fa aiyukan cigaban jahar baki daya.

Hukumar aikin hajji jahar Adamawa ta baiyana ranan da za a fara jigilan maniyatan jahar zuwa kasa mai tsarki.

Image
Hukumar aikin hajjin jahar Adamawa tace ta kammala dukkanin shirye shiryenta domin gudanar da aikin hajjin wannan shekara a kasa mai tsarki. Babban sakataren hukumar a jahar Adamawa Dr Salihu Abubakar ne yabaiyana haka a lokacin da yake jawabi a wurin rufe bita wanda hukumar ta shiryawa maniyata a yola. Dr Salihu Abubakar yaja hankalin maniyatan da sukasance a shirye domin hukumar ta kammala shirinta na fara tafiya kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajji. Shugaban hukumar ya kuma sanar da cewa za a fara jigilan maniyatan jahar Adamawa a ranan biyu ga watan shiddan wanan shekara. Shima a jawabinsa Jami in tsare tsaren aikin hajji karamar hukumar yola ta arewa Alhaji Ya u Gambo ya kirayi maniyatan da sukasance masuyin amfani da abunda suka koya a lokacinda ake yi musu bita domin ganin an samu nasaran gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali. Anashi bangaren Jami in tsare tsaren aikin hajjin karamar hukumar Madagali Alhaji Suleiman Yusuf ya shawarci maniyata da...

Kamfanin Dangote zaici gaba da taimakawa harkar ilimi a Najeriya.

Image
An kirayi iyaye da su baiwa ilimin yayan su muhimmanci. Babban manajan sashin aiyukan kamfanin dangote dake numan, Alhaji Bello Dan-musa ne yayi wannan kira yayin bukin ranan yara na bana, wanda ya wakana a sashin firamaren makarantan ma'aikatan dangote dake harabar kamfanin a Numan. Babban manajan sashin aiyukan kamfanin dangote, Alhaji Bello Dan- musa yace nasaran karatun duk wani da na da alaka da kokarin iyayen shi. Dan-mua yace Kamfanin dangote zai ci gaba da tallafawa ci gaban ilimi a matakin jaha da na kasa baki daya. Ya kara da cewa kamfanin zai ci gaba da kula da jin dadin malaman makarantan shi kamar yadda ya dace. Shugaban kungiyar malamai da iyaye da malaman makarantan wato PTA, mallam Lawan Adamu yace ware rana na musaman domin bikin ranar yara na da muhimma so sai har ma wa iyaye wadanda ke tallafa wa yaran a kulla yaumin. A cewar shi, koyawa yara sana'oin hannu zai taimaka musu bayan sun manyanta. A nata jawa, shugaban malaman makarantar, misis Grac...

Rudunan yan sanda a jahar Adamawa tasha alwashin ceto mutanen da wasu sukayi garkuwa da su a jahar.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta baza komarta domin ceto tare da zaukulo wadanda sukayi garkuwa da rev.Mike Ochigbo da pastor John Moses a fadin jahar baki daya. Rundunan ta baiyana hakane a wata sanarwa da ta fitar ta hanun kakakinta SP Suleiman Yahay Nguroje wanda kuma aka rabawa manema labarai a yola. Sanarwan tace dagajin labarin cewa anyi garkuwa da mutanen biyu sai kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurnin tura jami an tsaro domin shiga sako sako dama lunguna domin ganin an kama wadanda sukayi garkuwa da mutanen biyu harma da duk wanda yake da hanu ayin garkuwa da mutanen biyu. Sanarwa ta kuma kara da cewa kwamishin ya umurci dukkanin manyan jami an yan sandan dake fadin jahar da su dukufa wajen sanya ido domin ganin an samu nasaran cika hanu da wadanda sukayi garkuwa da mutanen. Kwamishin ya kuma tabbatarwa da cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyin al umma saboda haka rundunan na bukatan hadin kai da goyon baya daga...

Gidauniyar dake yaki da cutar yoyon fitsari a Najeriya ta kudiri aniya kawar da cutar.

Image
An baiyana cewa tsawon nakuda na daya daga cikin abunda ke haddasa cutar yoyon fitsari wanda hakan na jefa uwa da jarirai cikin mawuyacin hali. Shugaban gidauniya fistula a Najeriya Mallam Musa Isa ne ya baiyana haka a lokacinda yake jawabi danhane da ranar yaki da cutar ta yoyon fitsari ta duniya. Mallam Musa Isa yace matsalar samun jinkiri zuwa asibiti da kuma rashin wadatattun cibiyoyin kiwon lafiya musammanma a yankunan karkara suna taimakawa wajen haifar da cutar ta yoyon fitsari. Mallam Isa ya kara da cewa yanayin na talauci da karancin ilimi suma suna taka mahimmiyar rawa wajen musabbabin kamuwa da cutar don haka nema yake kira ga al umma musammanma magidanta da sukasance masu tallafawa matansu a koda yaushe musammanma wadanda ke dauke da juna biyu wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen kaucewa kamuwa da cutar ta yoyon fitsari. Harwayau gidauniyar ta fistula a Najeriya ta gabatar da kautukan yabo ga manyan likitoci da suka taka rawan gani wajen yaki da cutar ta...

An kirayi maniyata da sukasance masu taka tsantsan da kuma bin doka a lokacin aikin hajji. Suleiman Yusuf.

Image
An kirayi maniyata dake jahar Adamawa da sukasance masu bin dokoki kasar sudiya musammanma a lokacin aikin hajji wanda za a gudanar a wannan shekara domin ganin sun gudanar da aikin hajji karnabbe. Jami in tsare tsaren aikin hajji karamar hukumar Madagali dake jahar Adamawa Alhaji Suleiman Yusuf ne yayi wannan kira a zantawarsa da jaridar All Nur a yola. Alhaji Suleiman yace ya kamata kowane maniyaci ya kasance maibin dukkanin ka idodin aikin hajji da kuma dokar kasa mai tsarki wanda acewarsa hakan zaisa maniyaci yayi aikin hajji karbabbe. Ya kuma shawarci maniyatan da sukasance masu yin taka tsantsan wajen kula da kayakinsu dama jakkunansu domin acewarsa idan sukayi sakaci da jakkunansu wasu zasuyi anfani da wannan damar wajen cutar da su ta sanyamusu wasu kayaki da basu daceba. Don haka nema yace kada maniyaci ya bari wani yazo ya bashi ajiyar kayakin da bai sansuba ko yace rikemini wannan ina zuwa ko sako don ta haka wani yana iya basu kayakin da hwamnatin Saudiya ba...