Posts

An yaba da kamun ludayin Shugaba Bola Tinubu cikin kwanaki dari dayayi akan mulki.

Image
A yayinda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya cika kwanaki dari akan Mulki shugabancin Najeriya an yaba da kamun ludayinsa duba da irin yanayin matsalar rayuwa da ake ciki. Alhaji Adam Hassan Ibrahim shugaban kungiyar yan kasuwa a Arewacin Najeriya ne ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar Al Nur bayan godiya da yayiwa Allah madaukakin sarki yace shugaba Bola Tinubu ya taka rawan gani a fannoni daban daban a cikin kwanaki dari da yayi na farkon mulkinsa. Alhaji Adam Hassan yace shugaba Bola Tinubu ya fitar da tsare tsare da zasu kawo cigaban kasa musammanma a bangaren tattalin arziki da Kuma bunkasa harkokin noma da dai sauransu. Alhaji Hassan yace duk dacewa ana cikin wani yanayi da wahalar rayuwa Amman da yardan Allah komai zai daidaita domin kuwa a cewarsa bayan wahala akwai sauki. Ya kara dacewa ko a yanzu hakama shugaban kasa ya tafi kasar indiya domin halartan taron G ...

An yabawa gwamna Fintiri bisa aiyukan cigaban jahar da yayi a cikin kwanaki dari.

Image
A yayinda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya cika kwanaki dari akan Mulki bayan sake zabensa a wa adi na biyu. Hakan yasa jama a ke baiyana irin kamun ludayin gwamnan a cikin kwanaki dari. Sunday Wugari mataimakin na musamman na gwamnan kan harkokin jama a Yana daga cikin masu baiyana irin cigaba da aka samu a cikin kwanaki dari na farkon wa adin gwamnan na biyu. Sunday bayan ya godewa Allah ma daukakin sarki ya kuma yaba da irin aiyukan cigaba da gwamnan yayi a farkon kwanaki dari da yayi akan Mulki Wanda Kuma ya taka rawan gani wajen kawo zaman lafiya dama inganta tsaro a fadin jahar baki daya. Sunday yace ko a makon da ta gabatama gwamnan da yan majalisarsa sun amince da ware kudi da yakai Sama da nera bilyon daya domin magance matsalar ambaliyar ruwa a sashin anguwanin samunaka, Waru Jabbe da dai sauransu. Ga Kuma yadda gwamnan ya kudiri aniyar tallafawa Al umma jahar da ...

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ya bankodo wani yunkurin yin garkuwa da wani.

Image
A hobbasa da takeyi na dakile aikata yin harkuwa da mutane domin neman kudin fansa a fadin jahar Adamawa runduna yan sandan na jahar Adamawa ta takawa wasu masu yunkurin yin garkuwa da wani birki. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SPSuleiman Yahaya Ngurojene ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola wanda kuma aka rabawa manema labarai. Sanarwan ta baiyana cewa ofishin rundunan dake Karamar hukumar Gombe ne tare da hadin gwiwar sarkin bakan Gombi suka yi kokarin takawa wasu birkin yin garkuwa da wani mai suna Gideon Bitrus dake zaune a kauyen Jangra a karamar hukumar ta Gombi a jahar Adamawa. Kakakin yace an samu nasaran hakane biyo bayan bayanain sirri da aka samu wanda hakan yasa hukumar yan sandan batayi da wasaba wajen kai dauki wurin da ake zargi mafakan masu garkuwa da mutanen ne. Inda kuwa akayi nasaran tarwatsasu harma an gano wasu kayaki da ...

Majalisar dokokin jahar Gombe ta dakatar da zamanta sakamokon yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da kungiyar kwadigo keyi na kasa baki Daya.

Image
Rahotanni daga jahar Gimbe sun baiyana cewa yajin aikin gargadi na kwanaki biyu wanda kungiyar kwadigo N LC keyi a fadin kasan nan kungiyar a jiya ta murci majalisar dokokin jajar Gombe da ta dakatar da zamanta da zatayi domin tantance sabbin sunye kwamishinoni jahar da ka tura mata. Hakan na kunshene a cikin wata takarda da hukumar gudanarwar majalisar ta fitar inda tace majalisar ta dakatar da zamanta ne biyo bayan yajin aikin hargadi na kwana biyu da kungiyar kwadigo ta shirya wanda aka fara daga ran 5 zuwa 6- 9-2023. A rawaito cewa a safiya talatan nan ne dai majalisar ta shirya domin fara tantance sabbin mutane 17 a matsayin kwamiahinoni hakan yasa ala tilas majalisar ta dage zamanta domin yin mubaya a da yajin aikin gargadi da kungiyar kwadigo keyi na kwana biyu a fadan Najeriya. Rahotanni na cewa akasarin aiyukan gwamnati ya tsaya cik a cikin garin Gombe harma da cibiyoyin masu zaman K...

Yajin aikin gargadi na kwanann na biyu ya samu goyon bayan membobin kungiyar kwadigon a jahar Adamawa.

Image
A yayinda aka shiga rana ta biyu a yajin aikinda kungiyar kwadigo a Najeriya keyi a matsayin na gargadi Kuma rana ta kashe membobin kungiyar damq ma aikatu sun bada hadin Kai da goyon baya dangane da yajin aikin. Shugaban kungiyar kwadigo a Najeriya N L C shiyar jahar Adamawa kwamuret Emmanuel Fashe ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola dangane da yajin aikin game gari da kungiyar kwadigo keyi. Emmanuel Fashe yace kawo yanzu membobin kungiyar sun amsa kira domin kuwa a yanzu haka wurare irinsu tahashi, ma aikatu, sakateriya, Bankuna suna rufe Wanda acewarsa yajin aikin na gargadin yayi tasiri kenan. Ya Kuma shaidawa gwamnatin tarayya cewa bada sonsune suke shiga yajin aikiba Kuma bada sonsune suke yin zanga zangar lumanaba. Saboda haka yana mai Kiran gwamnati da tayi dukkanin abunda suka dace domin ganin ta biyawa ma aikatan bukatunsu. A vwarsa dai in har gwam...

Kungiyar Yan Jarida a Najeriya N U J shiyar jahar Adamawa ta yaba tare da taya murna ga gwamnan Finti cika kwanaki dari a wa adinsa na biyu.

Image
An yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagotancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa na mijin kokari da yayi wanjen gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa a kwanaki dari da yayi bayan sake zaben da akayi a wa adin na biyu. Kungiyar yan Jarida a Nijeriya N U J shiyar jahar Adamawa ne tayi wannan yabo a wata sanarwa da ta fitar a yola dauke dacsanya hanun sakatarenta Fidelis Jocthan. Sanarwa ta baiyana cewa gwamnan ya gudanar da aiyukan cigaba sosai a cikin kwanaki dari da yayi akan mulki a wa adinsa na biyu, wanda kuma mutane sun amfana da shirye shiryen gwamnati daban daban. Sanarwan ta yabawa gwamnan bisa yadda ya zabo kwamishinoninsa domin dorawa akan aiyukan da ya fara a wata adinsa na farko. Kungiyar tace yan jahar Adamawa kamar sauran yan Najeriya ne suma sun dandanin radadin janye tallafi maifetur da akayi wanda hakan yayi sanadiyar hauhawan farashin kay...

Dubun wani matashi ya cika a garin Ribadu dake karamar hukumar Fufore a jahar Adamawa

Image
Runduna yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama wani matashi mai shekaru ashirin da biyar da haifuwa bisa zargunsa dayiwa wata karamar yarinya fyade a garin Ribadu dake cikin karamar hukumar Fufore a jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Mataahin mai auna Abdu Agara dake zaune a Ribadu cikin karamar hukumar Fufore wanda ake zargi da yiwa wata yarinya karama fyade wanda tunin kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya bada umrnin gudanar da bincike, dangane da lamarin kuma da zaran an kammal bincike za a gurfanar dashi gaban kotu domin ya girbi abinda ya shuka.