A YAYINDA AKE DAF DA GUDANAR DA BIKIN MURNAN SHIGA SABUWAR SHEKARA KWAMISHINAN YAN SANDAN JAHAR ADAMAWA YA TURA JAMI AN TSARO DOMIN INGANTA TSARO A YAYIN BIKIN.
Biyo bayan shirye shiryen gudanar da bikin shugiwar sabuwar shekara da aka sabayi shekara shekara inda ake jiran gudanarwa a Unity Flyover Wanda ke daf da shelkwatan yan sandan ran 31-12-2024. hakan yasa rundunan Yan sanda tare da takwarorinta na tsaro sun turo Jami ansu zuwa wurin bikin dama sassan dake fadin jahar domin ganin an kammala bikin lafiya. Kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Saboda haka rundunan ta Sanara da sauya akalan zirga zirgan ababen hawa daga inda za a gudanar da bikin a ran 31-12-2024. da misalin karfe 4:00 na yamma. Wadanda zasuyi tafiya daga filin jirgin Saman kasa da kasa Aliyu Mustafa zuwa cikin garin Yola ana maishawartansu da su bi ta mahadar hukumar zuba jari Adamawa zuwa Target Junction zuwa dandalin Ribadau. Haka Kuma wadanda zasu bi titin Numan daga Dougirei da subi titin da zai kaisu zoo zuwa Tsohon kasuwa da zaibi zuwa ka...