Posts

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta kama mutane tara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Image
A kokarinta na kawar da aikata taddajci a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kamar mutane tara da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa biyo bayan farmaki da ta gudanar a sassa daban daban dake fadin jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace an samu nasaran kama wadanda ake zargi ne biyo bayan baiyanai sirri da suka samu Wanda hakan yasa kwamishinan Yan sandan jahar ta Adamawa Afolabi Babatola baiyi da wasaba inda ya tura Jami an tsaro domin kamosu daga maboyansu. Rundunan karkashin jagorancin kwamandan CRACK tare da hadin gwiwar mafarauta ne dai suka kai samamen tare da nasaran cika hanu da wadanda ake zargi. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana farin cikinsu da jin dadinsa dangane da na mijin kokari da Jami an tsaro sukayi wajen kama mutane ya kuma kirayesu da su Kara himma domin ganin an magance mats...

Hukumar NAFDAC a Najeriya tasha alwashin daukan matakin daina amfani da sanadiren dake canja launin fata a fadin Najeriya.

Image
Hukumar inganta abinci da magunguna a Najeriya NAFDAC tace nan gaba kadan zata fara tilastawa na daina yi da Kuma sayar da sanadaren dake canja launin fata a fadin kasan nan baki daya Babban darektan hukumar ta kasa farfesa Mojisola Adeyeye ce ta baiyana haka a wurin taron karawa juna sani Wanda hukumar ta shiyawa yan jarida a yankin arewa masaugabas dangane da hatsarin yin amfani da sanadaren dake sauya launin fata. a Maiduguri fadar gwamnatin jahar Borno. Babbar darektar Wanda darektan sashin sanadaren hukumar Dr Leonard Omokpariola ya wakilta tace an shiyar irin wannataro wa yan jarida a jihohin Kano, Enugu, Lagos, Abuja, Jos, Ibadan, da Kuma Port Harcourt. Tace hukumar ta lura cewa yin amfani da sanadaren dake canja launin fata yana barazana da lafiyar lamarin akalla mata a Najeriya Kaso Saba in da bakwai suna amfani da sanadaren . Farfesar tace hakan yasa suka nemi hadin kana yan jarida domin su wayarwa Al umma Kai dangane da illar da yin amfani da sanadaren dake canj...

An bukaci gwamnatin tarayya dana jahar su inganta tafkin geriyo Abdulrazak.

Image
An kirayi gwamnatin tarayya dana jiha da suyi dukkanin Mai yiwa domin yashe tare da inganta tafkin geriyo domin samun cigaban dama bunkasa tattalin arzikin jahar dama kasa Baki Daya. Sarkin ruwan tafkin na geriyo Alhaji Abdulrazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a lokacin da aka nude tafkin domin kama kifi da akeyi shekara shekara a tafkin dake cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Abdulrazak Abubakar yace kama kifi da akeyi Yana taimakawa sosai harma da Samar da sana o in dogaro da Kai ga matasa. Baya ga kamin kifin ana noma abubuwa da dama a baking tafkin na geriyo Wanda Kuma hakan yana kawo cigaban da dama a bangarori daban daban. Da wannan ne yaga ya Kamata su kirayi gwamnatin da masu ruwa da tsaki da su taimaka domin kaiwa tafkin dauk duba da irin matsaloli da suke fuskanga wani lokacima ruwa tafkin kafewa yakeyi.wanda Hakan yana janyo asara masu yawa. Da yake magane dangane da kama kifin kuwa sai Abdulrazak yace bana...

An baiyana matasa dacewa suna gudumawa da zasu iya bayarwa a tsakanin al umma Sheik Duguri.

Image
An kirayi matasa da sukasance jakadu na gari a tsakanin Al umma domin sune kashin bayan kowace Al umma a fadin duniya. Sheik Ibrahim Muhammed Dugri wakilin malamai Bauchi Kuma shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala Mai shelkwata a Jos shiyar Abuja ne yayi wannan kira a ganawarsa da manem labarai a yola. Sheik Ibrahim Muhammed yace matasa suna da rawa da zasu iya takawa wajen gudanar da aiyukan cigaban Al umma don haka ya Kamata Suma su bada tasu gudumawar wajen cigaba dama wanzar da zaman lafiya. Malamin addinin musulunci ya Kuma shawarci matasan da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin Al umma Mai makon hakama kamatayayi suyi dukkanin abinda zai hada kan Jama a dama cigaban zaman lafiya yadda ya Kamata. Ya Kuma kirayi matasa da su kaucewa yin bangan siyasa sukasance masu hada kansu da girmama shuwagabanin tare dayiwa iyaye biyayya Wanda acewarta Hakan zaisa su samu Albarka a rayuwarsu a Koda yaushe. Malamin ya Kuma baiyana cewa iyaye mata Suma su...

An taya Babbar Alkalain jahar Adamawa murna rundunan yan sandan jahar Adamawa.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taya Hon. Hapsat Abdulrahman murnan kasancewarta Babban Alkalain jahar Adamawa. Rundunan ta baiyana hakane a sakon taya murna dauke da sanya hanun kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje. A sakon murnan anjiyo Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yanaceawa nada Hon. Hapsat Abdulrahman a matsayin Babban Alkalain jahar Adamawa ta cancanta kasancewarta mace ta farko da zama Babbar Alkalain a jahar Adamawa. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa ya kuma tabbatar da cewa rundunan a shirye take tayi aiki kafada da kafada domin ganin an samu nasaran yakan ta addamci a fadin jahar baki daya. Don haka kwamishinan yace a madadinsa da sauran Jami an rundunan na taya maishari a Hapsat Abdulrahman murnan samun wannan mukami na Babbar Alkalin Alkalain jahar Adamawa. A ranan talatan nan ne dai gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya tabatarwa maishari a Hapsat Abdulrahman Babbar Alkalain jahar Adamawa bayan da aka ...

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta cafke mutene biyu da aka zargi dayin garkiwa da mutane.

Rudunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran cafke mutane biyu da ake zargi masu garkiwa da mutane ne a cikin karamar hukumar Mubi ta arewa a jahar Adamawa. Kakakin rudunan yan sandan na jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace rudunan ta samu nasaran kama mutane biyu da ake zargi ne biyo bayan bayanain sirri da aka samu dangane da wadanda ake zargi. Wanda Kuma hakan yada rundunan natayi da wasaba inda ta Kai samamai tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane dake cikin karamar hukumar Mubi ta arewa a jahar Adamawa. Rundunan ta dauki matakin hakane biyo bayan rahoton da suka samu na yin garkuwa da Aisha Ahmadu da maigidanta Ahmadu Muhammed tare da kashe Mai gidannata a kauyen Digil dake ciki karamar hukumar Mubi ta arewa. Wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa da yakai nera Milyon biyu da dubu dari biyar kafin su Sako mutane. Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi...

Kungiyar manoman auduga a jahar Adamawa ta taya gwamna Fintiri murnan cin zabe.

Image
Kungiyar manoman auduga a Najeriya shiuar jahar Adamawa tana Mai Yaya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan cin zabe a matsayin gwamna jahar Adamawa a zaben gwamna da aka gudanar a wannan shekara ta 2023. Shugaban kungiyar a jahar Adamawa Alhaji Muhammed Saleh Gwalan ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Alhaji Muhammed Saleh yace a madadin kungiyar da membobinta suna taya gwamna murnan lashes zaben da shi da mataimakiyarsa Farauta. Sanarwa ta Kuma kirayi Al ummar jahar ta Adamawa ta su baiwa gwamnan hadin Kai da goyin baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar Baki Daya. Harwayau sanarwa ta taya gwamnan murnan bikin karamar sallah da fatan Allah ya karbi ibada ya Kuma maimaita mana Amin. Alhaji Saleh ya Kuma kirayi daukacin Al umma jahar Adamawa da su cigaba da yiwa jahar dama kasa adu o I samar da zaman lafiya.