Posts

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta shiyar B tace tayi nasaran kama mutane akalla dari tara da saba in da bakwai a shekara ta 2022.

Image
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya N D L E A shiyar B Wanda ya kunshi jihohi Adamawa, Taraba da kuma jahar Gombe tace tayi nasaran kama mutane dari Tara da saba in da bakwai wadanda ake zargi da safaran miyagun kwayoyi a Yankin na B. Kwamadan hukumar a yankin na B Alhaji Idris Bello ne ya baiyana haka a lokacin da yake Zantawa da jaridar Al Nur a yola, dangane da irin nasarorinda hukumar ta N D L E A tayi a shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu a yankin. Kwamandan yace cikin wadanda aka kama dari tara da saba in da bakwai wadanda suka hada da mata an yankewa dari uku da sittin da biyar hukunci a yayinda dari uku da saba in da hudu kuma an basu shawarwari domin su daina ta ammali da miyagun kwayoyin. Alhaji Idris Bello ya kuma baiyana cewa hukumar tayi nasaran kama miyagun kwayoyi da nauyinsa yakai kilo grama milyon biyu da dubu dari bakwai da hamsin da bakwai da dari tara da saba in da uku. Wato 2,757,973. Da wannan ne kwamandan...

An yaba da shugabanci shugaban karamar hukumar Girei dake jahar Adamawa.

Image
An yabawa shugabancin karamar hukumar Girei dake jahar Adamawa Hon. Juda Amisa garkuwar Luru tafida. Tambo. bisa yadda yake gudanar da aiyukan cigaban karamar hukumar dama cigaban karamar hukumar. Muhammed Muratalan ya yi wannan yabo a lokacinda ya zantawa da jaridar All Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Muhammed Murtala yace Him. Juda ya gudanar da aiyukan cigaban Al ummar karamar hukumar ta Girei a bangarori daban daban da suka hada da gina asibitoci, makarantu, Bohol Bohol, hanyoyi, bunkasa harkokin noma, da kiwo zaman lafiya da dai sauransu. Murtala ya kuma baiyana cewa Juda mutumne da ya san makaman shugabanci saboda yayi kansila har sau biyu ya rike mukamin shuhaban majalisar kasinlolin karamar hukumar ta Girei, ya kuma yi mataimakin shugaban karamar hukumar Girei haka kazalika ya yi shugabancin karamar hukumar Girei sau biyu, saboda haka ya kware wajen gudanar da shugabanci da kuma gudanar da aiyukan cigaban Al ummah. Don haka n...

An bukaci iyaye su kara kaimi wajen tura yaransu islamiyoyi.

Image
An ja hankalin iyaye da su maida jankali wajen tura yaransu makarantu domon koyon karatun Al qur ani maigirma domin ganin an samu cigaban karatun al qur ani a tsakanin yara baki daya. Alhaji Sadiq Umar Daware ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin bikin kammala gasar karatun Al qur ani maigirma wanda Gaskiya TV afirka ta shirya a yola. Alhaji Sadiq Daware shinema shugaban taron yace koyar da yara karatun Al qur ani tun suna yara yana da matukan muhimmanci don haka yakamata iyaye su tashi tsaye wajen baiwa yaransu ilimin karatun Al qur ani domin samun cigaban addinin musulunci. Ya kuma yabawa kungiyar ta gaskiya TV da ta shirya wannan gasa kuma ya kirayi sauran kungiyoyin addinin musulunci da su cigaba da shirya irin wannan gasa wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen bunkasa ilimin addini da ma karatun Al qur ani maigirma. Ya Kara jaddada goyon bayansa a duk lokacin da aka bukaci taimakonsa tare da shawartan al umma musulmai da sukasance masu...

Kungiyoyi dari biyar ne suka kudiri aniyar ganin Alhaji Atiku Abubakar yayi nasara a zabe mai zuwa.

Image
A kalla kungiyoyi Nagoya bayan Atiku dari biyar ne sukayi rijista domin ganin Alhaji Atiku Abubakar yayi nasara a Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Ko odinatan Atiku Mandate na kasa Alhaji Sa idu Komsari ne ya baiyana haka a wajen taron shuwagabain kungiyoyin da aka gudanar a yola. A taron dai kungiyoyin sunyi Alwashin ganin dan takaran shugaban kasa a jam iya P D P Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a zabe mai zuwa. Kungiyoyin dai sun hada Kansu tare da nuna jindadinsu da shirya wannan taro Wanda hakan ya nuna cewa wazirin Adamawa zai kai ga samun nasara. Don haka Alhaji Sa idu Komsiri ya kirayi kungiyoyin da su tabbata sunyi aiki kafada da kafada da sauran kunyoyin domin ganin an samu nasara a Babban zaben. Ya kuma kirayin yan Najeriya da su hada kai su baiwa Alhaji Atiku Kuri u wanda hakan zai taimaka ya samu damar lashe zaben sjekara ta 2023. An dai gudanar da jawabai daban daban a ...

An baiyana irin muhimmanci da karatun Al qur ani mai girma yake dashi a tsakanin al ummah musulmai.

Image
An kirayi Al ummah musulmai da su kara himma wajen gudanar da karatun All qur ani kai girma domin samun cigaban addinin musulunci yadda ya kamata a tsakanin Al ummah musulmai baki daya. Alhaji Sadiq Umar Daware ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bikin rufe gasar karatun Al qur ani mai girma wanda kungiyar gaskiya TV Africa shiyar jahar Adamawa ta shirya a yola. Alhaji Sadiq Daware wanda shine shugaban bikin yace karatun Al qur ani dama karantarwa yana da mutukan muhimmanci a tsakanin Al umma musulmai don haka akwai bukatan al umma musulmai sukasance masu runguman karatun Al qur ani domin samun daman yada addinin musulunci. Alhaji Daware ya kuma yabawa kungiyar ta Gaskiya TV bisa shirya wannan gasar karatun al qur ani mai girma ya kuma yi fatan zasu fadada aiyukansu har zuwa nahiyar Afirka baki daya. Ya kara kira ga al umma musulmai musammanma kungiyoyin addinin musulunci da suyi kasance masu shirya gasar karatun al qur ani ma...

An horar da dalube harkokin wasanni daban daban a jahar Taraba.

Image
Daga Sani Yarima Jalingo. An shawarci musammanma dalube da sukasance masu neman ilimin wasan badminton domin su zama masu gudanar da irin wasanin a fadon duniya. Darectan wasannin jahar Taraba George Shitta ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake jawabi a wurin bikin kamala horar da daluben sakandare wasan badminton da aka dauki tsawon kwanaki uku anayi a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba. Dalube tamanin daga makarantun sakandare tamanin ne dai da suka da gwamnati harma da masu zaman kansu suka samu haron wasanni daban daban akalla ashirin da hudu. Shitta ya shaidawa manema labarai cewa wata kungiya mai zaman kanta wato kungiyar bunkasa wassani da ilimantarwa a cikin al umma CSED tare da hadin gwiwar sashin wasan badminton a jahar Taraba ne suka dauki nauyin. Yace sun dauki matakin horan da daluben ne domin zaburan da matasa dama bunkasa harkokin wassani a jahar ta Taraba. Darektan ya kuma yaba da yadda kung...

Kungiyar Attarahum Faundation ta kaddamar da sabbin suwagabanninta nq kananan hukumomi.

Image
Kungiyar Attarahum Faundation dake jahar Adamawa ta kaddamar da shuwagabaninta na kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar Adamawa. An dai gudanar da taron kaddamawan ne a yola ta kudu a jahar Adamawa, wanda ya samu halartan Al umma dama da suka hada da yan siyasa da dai sauransu. Da yake jawabin maraba shugaban gidauniyar ta Attarahum Foundation a jahar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ya baiyana dalilinsu na kafa wannan gidauniya domin taimakon kai da kai harma da taimakawa marassa galihu, marassa lafiya,marayu, gajiyayyu da dai sauransu. Wanda kuma hakan yasa suka ga ya dace su fadada gidauniyar zuwa kananan hukumomi wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cimma burinsu na taimakawa al umma baki daya. Don haka nema ya kirayi al umma da sukasance masu kafa irin wannan gidauniyar domin taimakawa jama a tare da shawartan masu hanu da shuni da suma su bada tasu gudumawa wajen tallafawa jama a. Malam muktar Dayyib ya yabawa yar takaran gwamnat...