Posts

Sama da mutane dubu ashirin nedai zasu samu tallafi wadanda ambaliyar ruwan bara ya shafa a jahar Yobe.

Image
A kalla mutane dubu ashirin da biyar wadanda ambaliyar ruwar bara ya shafa zasu amfana da tallafi daga gwamnatin tarayya a jahar Yobe. Da yake kaddamar da rabon kayakin a gidan gwamnati dake Damaturu. Gwamna Mai Mala Buni yace jahar Yobe tana daya daga cikin jihohi da suka dan dana kudarsu a nangaren ambaliyar ruwa lamarin da yayi sanadiya mutuwar mutane sama da saba in. Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA tace tana iya kokarinta domin ganin an tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a fadin kasar tun daga shekara ta 2022. domin ganin an cike gibin da aka rasa sakamokok ambaliyar ruwan a fadin Najeriya. Gwamnan yace sama da magidanta arba in ne lamarin ya shafa tare da lalata hanyoyi da dama. Gwamna Mai Mala ya yabawa gwamnatin ta tarayya bisa taimakon da tayiwa ambaliyar ruwa ya shafa a jahar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye ta...

Gwamnatin jahar Adamawa ta kafa kwamitin da kula da rarraba kayakin tallafi was Al ummar jahar ta Adamawa.

Image
Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Finti ya kafa kwamiti Mai mutane ashirin Wanda zai kula tare da rarraba kayakin tallafi domin ragewa Al ummar jahar radadin wahala da aka shiga sakamokon cire tallafin maifetur. Gwamna Ahmadu Umaru Finti ya baiyana haka ne a cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labarain gwamnan Humwashi Wonosikiu da ya fitar Wanda aka rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Kwamitin dai sun hada kungiyoyi, hukumomi,dama daidaikum jama a Wanda sune zasu kula da Kuma rarraba kayakin tallafin wa Al ummar jahar. Acewar sanarwan dai karon farko za a rarraba kayakin abinci da suka hada da hatsi. Kuma a ranan Alamis 24-8-2923 ne za rantsar da kwamitin da misalin karfe goma sha Daya na safe a dakin taro na gidan gwamnati dake nan yola. Wanda Kuma sakataren gwamnatin jahar ta Adamawa. Awwal D Tukur zai kasance shugaban kwam...

An bukaci hadin Kai a tsakanin shuwagabanin da wadanda ake mulka domin magance matsalar cin hanci da rashawa.

Image
An bukaci kyakkawar gwamnatin da adalci domin kawar da matsalar cin hanci da rashawa a tsakanin Al umma. Farfesa Abdullahi Bashir ya baiyana haka a lokacin da yake gabatar da lekca a wurin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki Wanda kungiyar wadata Media Advacacy tare da hadin gwiwar Fombina FM suka shirya a yola. Farfesa Abdullahi Bashir yace Yana da muhimmanci gwamnati ta maida hankali wajen yin adalci da kyautatawa jama a a wani mataki na magance matsalar cin hanci da rashawa dama Samar da zaman lafiya. Yace Babban matsalar da ake samu a yanzu shine rashin fahintar Juna a tsakanin gwamnati da wadanda ake mulka don haka akwai bukatar gwamnatin tayi dukkanin maiyiwa domin inganta aiyukanta ga Al umma Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen rage radadin cin hancin a tsakanin Al umma. Tunda farko a jawabinsa Malam Zubairu Idris AbdulRa uf yace rashin kyakkawar shugabancinse da wasu keyi yasa ake fuskantar matsàlolin da dama ciki harda cin hanci d...

An yabawa masuyiwa kasa hidima a jahar Taraba.

Image
Daga Sani Yarima Jalingo. Gwamnan jahar Taraba Dr Agbu Kefas ya yabawa masuyiwa kasa hidima bisa kokarinsu na kirkiro tare da koyon sana o in dogaro da Kai karkashin shirin nan na koyar da kananan sana o I da cigaba wato (SAED). Dr Àgbu Kefas ya baiyana haka ne a wajen bikin Bude wayarwa masuyiwa kasa hidima Kai na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku na rukunin A Wanda aka gudanar a sansanin masuyiwa kasa hidima na dindindin dake Sibre, a karamar hukumar Ardo Kola dake jahar Taraba. Gwamnan Wanda kwamishinan cigaban matasa da wasanni Ambasada Joseph Joshua ya wakilta yace masuyiwa kasa hidima sunyi rawan gani Kuma abun a yabane saboda sun samarwa kansu aiyukan da zasu dogara da kansu. Ya Kuma kirayesu da sukasance masu kyakkawar dabi a da Kuma bin doka da oda a Koda yaushe tare da yin tsare tsaren da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki a fadin jahar baki Daya. ...

Gwamnatin jahar Yobe ta lashi takwabin inganta tsaro a fadin jahar.

Image
Gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni yace gwamnatinsa zata cigaba da baiwa bangaren tsaro da ma walwalan masuyiwa kasa hidima musammanma wadanda aka turo hajar muhimmanci domin samun cigaba. Gwamna Mai Mala Buni ya baiyana haka ne a wurin bikin tantsar da masuyiwa kasa hidima wato Rukunin B na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku Wanda bikin ya gudana a sansanin masuyiwa kasa hidima dake Dazigau a karamar hukumar Nangere a jahar ta Yobe. Gwamnan wanda mai taimaka masa na musamman aka koyar da sana o i da samar da aikikyi Abdullahi Bego ya wakilta ya baiyana cewa tunin aka umurci hukumomin tsaro da shuwagabanin al umma su tabbatar da ingancin muhallin masuyiwa kasa hidima. Ya kuma kirayi masuyiwa kasa hidima da sukasance masu gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin samun cigaban sansanin. ...

An rantsar da sabbin shuwagabanin kungiyar Yan kasuwa a jahar yobe

Image
Daga Ado Yaro Gashuwa Damaturu. Hadakar kungiyoyin yan kasuwa dake jahar Yobe sun gudanar da zaben sabbin shuwagabanin kungiyar wadanda zasuja ragamar kungiyar na shekaru hudu masu zuwa. An dai gudanar da zabenne a Dakin taro dake cikin garin Damaturu fadar gwamnatin jahar Yobe. Da yake jawabi a lokacin zaben shuhaban kwamitin shirya zaben Alhaji Ibrahim Muhammed Bello ya kirayi membobin kungiyar da sukasance masuyin aiki tukuru domin cigaban kungiyar a fadin jahar baki daya. Alhaji Ibrahim Muhammed Bello ya yabawa membobin kungiyar bisa hadin kai da suka bayar a wajen zaben wanda hakan yasa aka gudanar da inganceccen zaben. Kuma yayi amfani da wannan damar domin yabawa gwamnatin Mai Mala Buni bisa kokarinta na baiwa kungiyar hadin kai harma da taimakawa kungiyar dama yan kasuwa dake fadin jahar. ...

Duba da yanayi na matsalar rayuwa da ake ciki anshawarvi Al umma da su maida lamuransu ga Allah Madaukakin Sarki.

Image
An shawarc al umma da su maida dukkanin lamuransu ga Allah madaukakin sarki domin neman saukin rayuwa duba da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a yanzu biyo bayan cire tallafin maifetur wanda shugaban kasa Bola Tinubu yayi. Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji Gambo Jika yace yakamata da zaran an shiga wani yanayi da tsadar rayuwa to kamatayayi a maida hankali wajen yin adu o i da gudanar da aiyukan Alheri dimin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen wahalar rayuwa da ake ciki a halin yanzu. Ya kuma kirayi gwamnati da itama ta yi dukkanin abunda suka dace domin ganin ta tallafawa al umma saboda suma su samu saukin rayuwa kasancewa itace uwa mabada mama. Don haka ya kamata gwamnatin tarayya dana jahar da su tashi tsaye wajen tallafawa ja...