Posts

Bunkasa Noma: mata hamsin sun samu tallafi kan noma daga kamfanin Dangote a jahar Adamawa.

Image
Kamfanin Dangote dake Numan ta kaddamar da shirin tallafin Naira miliyan biyu da rabi wa mata manoma da dake ƙauyukan da ke kewaye da ita. A jawabin shi yayin bukin kaddamar wan da ya wakana a harabar kamfanin, gwamnan jahar Adamawa  Umaru Fintiri ya gode wa kamfanin da yadda ya  yunkura domin saka mata cikin shirye shiryen ya na bada tallafi. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya samu wakilcin Komishiniyar Ma'aikatar harkokin mata  Neido Geoffrey Kofulto yace mata suna da jajircewa da sa kai a dukkan abun da aka saka su, shi yasa kamfanin Dangote ya ba su wannan dama domin tallafa musu.   Gwamnan ya shawarci matan da suyi amfani da wannan kudin ta hanyar da aka tsara su saboda a samu sakamakon da zai kara bude kofa domin wasu ƙarin matan su ma su amfana. Fintiri ya godewa sarakunan gargajiyan yankin da yadda suke baiwa Kamfanin goyon bayan tafiyar da ayyukan ta da ma sauran shirye shirye wa mutanen su. A nashi jawabi, daya daga cikin manyan jagororin kamfanin Dangote...

Kungiyar Fityanu shiyar karamar hukumar yola ta arewa ta kammala horon da tayiwa Yan agajinta.

Image
  Kungiyar Fityanu shiyar karamar hukumar yola ta arewa ta gudanar da bikin kammala horo da tayiwa Yan agajinta na watanni shida domin karfafa aiyukansu wajen taimakawa Al umma. A jawabinsa a wajen taron Modibbo Safiyanu Iya Runde wakilain malamai jahar Adamawa Wanda Malam Hayatu iya ya wakilta ya baiyana Jin dadinsa tare da cewa aikin agaji abune da yake da mutukan muhimmanci don haka Yan agajin sukasance masu taimakawa jamma a domin kaucewa shiga matsala. Modibbo Safiyanu ya Kuma kirayi Al umma musulmai da sukasance masu Neman ilimin addini da na zamani a Koda yaushe domin acewarsa ilimi shine ginshikin duk abinda zai kawo cigaba dama zaman lafiya  da dai sauransu. Ya Kuma shawarci wadanda aka horar din da suyi amfani da abinda aka koya musu domin ganin an samu cigaban aiyukansu da ma jinkai a tsakanin Al umma baki Daya. Shima da yake nashi jawabi darektan Yan Agajin Fityanu a jahar Adamawa Mallam Sa idu Modibbo Buba ya baiyana cewa an shirya horon ne domin akarawa Yan agaji...

Gwamnatin jahar Jigawa ta aiyana ranan talata a matsayin hutu domin bada damar gudanar da bikin cika shekaru 33 da kirkiro jahar.

Image
  Gwamnatin jahar Jigawa ta aiyana ranan talata 27-8-2024 da ya zama ranan hutu ga ma aikata jahar domin gudanar da bikin cika jahar shekaru 33 da uku da kikiro jahar ta Jigawa. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa daga Jami in yada labarain ofishin shugaban ma aikatan jahar  Isma Ibrahim Dutse ya fitar a jahar. A sanarwar an jiyo shugaban ma aikatan jahar Alhaji Muhammed K Dagaceri na Kiran Al ummar jahar suyi amfani da wannan lokacin wajen yiwa jahar ta Jigawa dama kasa adu o I domin Samar da zaman lafiya dama cigaba. Sanarwan ta Kuma baiyana cewa dafatan dukkanin ma aikatan jahar zasu Yi amfani da ranan wajen godewa Allah madaukakin sarki taro da adu ar Allah ya kawo zaman lafiya hadin Kai dama cigaba a jahar Jigawa. Ya Kuma kirayi jama a da su yiwa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a wasu sassan jahar Adu a,  lamarin da yayi sanadiyar rasa rayuka dukiyoyyi masu yawa. A shekara ta 1991 ne dai aka kirkiro jahar Jigawa karkashin mulkin soja Gen. Ibrahim Badamasi Babangid...

Yan sanda biyu sun gamu da ajalisu tare da jikkata uku a wani hari da aka Kai akan Jami an Yan sanda a Abuja.

Image
  Jami an Yan sanda biyu ne suka rasa rayukansu a yayinda uku suna cikin wani yanayi na jikkata tare da cinnawa motoci Yan sandan wuta, sakamokon hari da ake zargin mabiya darikar shiya ne suka kaiwa Yan sanda a dai dai lokacinda suke gudanar da aiyukansu a shingen binciken ababen hawa dake mahadar wusai a birnin tarayya Abuja. Kakakin rundunan. Yan sandan Abuja SP Josephine Adeh ta baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a madadin kwamishinan Yan sandan na Abuja. Kwamishinan Yan sandan Abuja Benneth C Igweh yayi Allah wadai da wannan hari na rashin tausayi da aka kaiwa Yan sanda tare da yin alkawarin hukunta duk Wanda aka samu da laifin akata haka inda yace kawo yanzu komai Yana tafiya dai dai a inda lamarin ya faru.

Sarkin Ningi ya rasu Yana da shekaru 87.

Image
 Rahotanni daga jahar Bauchi na cewa Allah yayiwa Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammed Danyaya tasuwa. Basaraken ya rasune a wani asibiti dake Kano bayan kwanaki biyu da ya dawo daga duba lafiyarsa a kasar Saudiya. Kuma ya rasu Yana da shekaru 87 da haifuwa. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa daga sakataren fadar Alhaji Usman Sule magayaki Ningi. Tare da baiyana cewa za ayi jana izarsa da misalin karfe 4:00 na yamma a fadarsa dake Ningi.A Ladin nan 25-82024.

Sabon kwamandan Rundunan tsaro na Civil Defence a jahar Adamawa ya kama aiki.

Image
  Rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula wato Civil Defence shiyar jahar Adamawa ta marabci  sabon kwamandan ta Idris D Bande Wanda tuninma ya fara aiki a hukumance Jin kadan da karabar ragamar shugabancin rundunan daga Wanda ya gada Ibrahim Mainasara. An dai bikin marabtar sabon kwamandan ne a shelkwatar rundunan ta NSCDC dake nan Yola. Kakakin rundunan. ta NSCDC a jahar Adamawa DSC Nyako Amidu Baba ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Fadar gwamnatin jahar Adamawa. Sabon kwamandan dai an sauya masa wurin aiki ne daga yankin B dake jahar Kaduna Wanda ya maye gurbin Ibrahim Mainasara Wanda yayi aiki na tsawon shekara Daya da watanni uku Kuma shine kwamandan rundunan na 15 a jahar Adamawa. A lokacinda yake mika ragabab shugabancin rundunan ga sabon kwamandan Ibrahim Mainasara ya kirayi dukkanin Jami an rundunan da su baiwa sabon kwamandan cikekken hadin Kai da goyon baya domin tabbatar da ganin cewa rundunan ta cigaba da gudanar da aiyukan ...

PCRC dake Jambutu sun junjinawa rundunan yan sandan jahar Adamawa.

Image
  Al umma dake taimakawa rundunan Yan sanda wato PCRC shiyar anguwar Jambutu ta yabawa rundunan Yan sandan jahar Adamawa  bisa kokarinta na inganta tsaro a lokacin zanga zangan kasa da ya gudana a fadin Najeriyar. Shugaban PCRC dake Jambutu Alhaji Adamu Jingi Wanda akafi sani da Mai hange ne ya yi wannan yabo a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Adamu Jingi yace rundunan yan sandan ta taka rawan ganin wajen inganta tsaro a lokacin zanga zangan a jahar Adamawa saboda haka rundunan ta cancanci yabo saboda irin wannan na mijin kokari da rundunan Yan sandan tayi. Alhaji Adamu ya Kuma baiyana cewa  yabon Gwani ya zama dole domin rundunan yan sandan karkashin jagoranci kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris tayi kokari wajen kare rayuka dama dukiyoyin Al umma a fadin jahar Adamawa. Adamu Jingi ya Kara da cewa PCRC dake shiyar Anguwar Jambutu a shirye take ta baiwa rundunan Yan sandan hadin Kai da goyon baya domin ganin ta sa...