Posts

Showing posts from July, 2023

Mutane shida ne suka mutu biyo bayan hari makami Mai lizami da Rasha takai Ukraine.

Image
Akalla mutane shida ne suka gamu da ajalinsu ciki harda wata yarinya yar shekaru goma da haifuwa tare da mahaifiyarta biyo bayan harin makami mai lizami da Rasha ta kai a garin kryvyi Rih dake kasar Ukraine. Ministan harkokin kasashen wajen kasar ta Ukraine yace baya ga watanda suka mutu mutane sittin da tara ne suka samu rauni sakamokon harin da aka kai a wani gini dake wata Jami a a litinin din nan. Gwamnan yankin Serihiy Lysak ya aiyana ranan ta yau da ya zama ranan zaman makoki saboda wadanda suka rasa rayukansu. Garin da aka kai harin da na mahaifar shugaban kasan na Ukraine Volodymyr Zalensky. Ko a ciki watan shida na wannan shekara Rashan ta kai hari akan ginai ginen fararen hula wanda yayi sanadiya mutane 11tare da jikkata mutane 28. SANARWA. SaNARWA. SANARWA Hukumar makarantar NAFAN Academy na sanar da al umma cewa ta fa

Taliban ta Kona kayakin wakoki a Afghanistan.

Image
Kungiyar Taliban a kasar Afghanistan wanda itace ma take jagorantar gwamnatin kasar ta kona kayakin wakoki da dama wadanda kudadensu ya kai dubbain daloli. Taliban din dai tace ta dauki matakin haka ne saboda bata tarbiya da masu wakokin keyi don haka taga bata da zabi illa ta kona kayakin wakokin. Lamarin dai ya farune a yammaci lardin Herat dake kasar ta Afghanistan. Tun a shekara ta 2021 ne lokacinda Taliban din ta hawmilki kasar ta dakatar da aiyukan mawakan a bainan jama a . Ahmed Sarmast Jami in ne a cibiyar bunkasa harkokin waka yace wannan wani matakine na murkushe harkokin waka. Makarantu dake koyar da wakokin dai sunyi shiru a karkaahin mulkin Taliban .

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace tana tsare da mutane sama da dari wadanda ake zairgi da wawushe kayakin abinci.

Image
Runduan yan sandan jahar Adamawa tace ta kama mutane da dama wadanda ake zargi da hanun a cikin wawushe kayakin abincin gwamnati dana al umma. A wata sanarwa da kakakin runduna yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya aikewa manema labarai a yola, na cewa rundunan ta samu nasaran kama mttane akalla dari da goma (110) wadanda ake zargi da faffasa runbuna Adana abincin gwamnati tare da kwashe kayakin. Da wannan ne rundunan ke gargadi al umma da su kaucewa dukkanin abinda zai haifar da matsaloli a tsakanin Al umma. A cewar kakakin rundunan yan sandan rundunan a shirye take ta saka kafar wando daya da duk wanda yayiwa doka karan tsaye.

Shugaban kasa zaiyiwa Yan Najeriya jawabi.

Image
yau Ltinin 31-7-2023 ne ake saran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yiwa al ummar kasa jawabi ta misalin karfe bakwai na yammaci. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shuhaban kasa Dele Alake ya fitar a safiyar yau litinin. Sanarwan dai na umurtan kafafen yada labarai da su watsa jawabin kai tsaye da zaran shugaban kasa ya fara jawabi. Duk da cewa ba asan ko akn minene shugaban zaiyi jawabiba amman y jawabin yazo kan gaba duba da irin wahalar rayuwa da ake ciki sakamokon cire tallafin maifetur. NAFAN COLLEGE OF SCIENCE AND HEALTH TECHNOLOGY Kwalejin dake haras da kiwon lafiya kimiya da fasaha dake Unguwar Jambutu a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Kwalejin ta bude tare da fara karantar da kwasakusai a bangarorin kiwon lafiya da

An gudanar da gasan karatun Al kur ani mai girma a tsakanin marayu a jahar Adamawa.

Image
A karon farko an shiryawa maru gasara karatun Al kur ani mai girma domin ganin an samu cigaban karatun Al kur ani a tsakanin Al umma. Da yake jawabi a wurin bikin rufe gasara karatun Al kur ani wanda aka gudanar a makarantar FOMWAN dake yola. Mallam Musa Kaduna yace wannan shine karo na farko kenan aka shirya irin wannan gasar ga marayu domin ganin an karawa marayun kwarin gwiwar haddar karatun Al kur ani mai girma. Shima a jawabinsa bako mai jawabi Mallam Ali Mamman ya baiyana ahirya irin wannan gasa yana da matukan muhimmanci da wannan nema yake kira ga mawadata da suyi koyi da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi wajen taimakawa marayu, wanda avewarsa hakan zai kara musu kwarin gwiwar cigaba da karatu yadda ya kamata. Shugaban

Kungiyar kwadigo a Najeriya ta bugi kirjin shiga yajin aikin kasa baki Daya.

Image
Gwamnatin tarayya da wakilan kungiyoyin kwadago za su sake ganawa a ranar litinin din nan domin sake lalubo mafita aka tankiyar da ke tsakaninsu. Kungiyar ta kwadago ta na shawarta alummar Najeriya su tanadi Abinci da magunguna da sauran Kayan amfanin yau da kullum saboda yajin aiki da za a tsunduma na tsawon mako guda saboda cire tallafin man fetur. Ta ce wannan gargadi ya zama wajibi saboda yajin aikin zai dakatar da duk wasu mahimman ayyuka da suka hada da zirga zirgar harkokin sufuri da makarantu da bangaren kula da lafiya, da kasuwanci da sauran Ayyuka masu mahimmanci. Mataimakin shugaban kungiyar na kasa Chris Onyeka, ya tabbatar da haka a lokacin da yake magana da manema labarai a Abuja, inda ya ce akwai Bukatar Yan Najeriya su takaita zirga zirgansu saboda kaucewa duk wata cikas da za su iya fuskanta.

Cibiyar bunkasa harkokin harsuna da Al adu a Najeriya ta kawo karshen shirye shiryenta na shekara ta 2023.

Image
Cibiyar bunkasa harsunan Najeriya ta kasa NICO tace ta kammala shirye shiryenta na shekara ta 2023 dangane da gangamin wayarwa al umma kai dangane da harsuna a jahar Adamawa. An dai gudanar da bikin kammala shirye shiryen ne a Barikin yan sanda dake nan yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Darektan cibyar ta NICO a shiyar Arewa masau gabas Mrs Jane Anigala wanda shugaban sashin gudanarwar cibiyar Abdullahi Ndribita ya wakilta yace tun a ahekara ta 2017 ne cibiyar ta fara gangamin wayarwa jama a kai dangane da harsunan a Najeriya. Ya kuma baiayana cewa cibiyar na da shiyoyi har sha shida a shiyoyi ahida dake fadin Najeriya.harma da birnin tarayya Abuja. Abdullahi ya baiyana damuwarsa dangane da yadda ake samun koma naya a bangaren cigaban harsunan Najeriya kuma abun takaicinma shine yadda wasu iyaye

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ya tabbatar da kama mutane 25 wadanda ake zargin da hanu a kwashe kayakin abinci a rbunan gwamnati.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tabbatar da kama tare da tsare mutane a kalla ashirin da biyar Wanda ake zargi da hanu a cikin fasa tare da kwashe kayakin abinci dama sauran kayakin a runbun a abincin na gwamnati jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar ta Adamawa SP Suleiman Yahay Nguroje ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da manema labarai a yola. SP Suleiman Yahaya Nguroje yace rundunan satayi dukkanin maiyiwa domin maido da dkkanin kayakin da aka sace. SP Suleiman ya kuma tabbatarwa al ummar jahar Adamawa cewa rundunan zatabi dukkanin ka idodi da suka dace kamar yadda gwamnatin jahar ta baiyana amman kuma jama a su sani rundunan zata shiga kafar wando daya da duk wanda yayiwa doka karen tsaye. A nashi bangaren Shuguban hukumar agajin gaggawa ta kasa dake jahohin Adamawa da Taraba Landan Ayuba ya

Gwamnatin jahar Adamawa ta sanya dokan hana ziga zirga na sa o I 24.

Image
Wasu gungun matasa a jahar Adamawa sun fasa wani siton abinci tare da kwashe kayakin da dama bisa zargin gwamnati da ajiye abinci ba tare da rarrabawa Al ummaba a cewar matasan. Biyo bayan wannan hatsaniya dai gwamnatin jahar ta Adamawa ta sanya dokan hana fita na sa o I ashirin da hudu Wanda ya fara aiki nan take. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai gwamna finti Humwashi Wonosikiu ya fita Kuma aka rabawa manema labarai a yola. Sanarwan tace biyo bayan da gungun matasa da sukayi cincirindo a madainain ajiye kayakin abinci ya zama dole minsanya dokan domin bada kariya ga kayakin jama a dama rayukansu a cewa gwamna Ahmadu Umaru Finti.na jahar Adamawa. Sanawar ta Kuma baiyana cewa sai wadanda ke da aiyuka na musamman ne suke da damar gudanar da zirga zirga a lokacin dakan. Kawo yanzu tunin aka rufe Babbar

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin daki aiyukan masu fasa shaguna.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tura Jami an yan sandan kwantar da tarzoma a wani mataki na dakile aiyukan wasu gungun matasa dake fasa shagunan ajiye kayakin abinci dake fadin jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwan tace kwamishinan yan sandan Jahar Adamawa Afolabi Babatola ya umurci Jami an yan sandan kwantar da tarzoma dama sauran hukumomin tsaro da su tabbata kowa yabi dokan da gwamnatin jahar ta kafa na hana zirga zirgan na tsawon sa o i ashirin da hudu.

Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar yola ta arewa takudiri aniyar koyarwa yaran sanin watannin addinin Musulunci.

Image
majalisar harkokin addinin musulunci a karamar hukumar yola ta arewa ta sha alwashin ganin ta wayarwa dalube Kai dangane da sanin watannin addinin musulunci dama shekaran. Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a yola ta arewa Alhaji Abdullahi Abubakar Butu ne ya baiyana haka a lokacinda yake amsa tambatoyi daga manema a yola. Alhaji Abdullahi Butu yace yanzu haka suna Shirin rarrabawa makarantun Islaniyoyi takardu wadanda suke dauke da watannin addinin musulunci dama kalandar ta addinin musulunci. A cewarsa dai karantar da yara sanin watannin addinin tun suna matakin islamiya zai taimaka wajen wayarwa jamma a Kai dangane da watannin na addinin musulunci. Ya Kuma kirayi iyayen da Suma su bada tasu gudumawar wajen fahintar da yaran sanin watannin addinin musulunci tun suna yara domin samun cigaban addinin musulunci.

An shawarci Al umma Musulmai dangane da amfani da kalandar addinin Musulunci.

Image
An kirayi Al umma musulmai da sukasance suna dai hankali wajen amfani da kalanda addinin musulunci a Koda yaushe domin samun cigaban addinin musulunci yadda ya kamata. Mallam Modibbo Ahmadu Kulangu ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin wani taron da kungiyar Munazzama ya shirya dangane da sabuwar shekaran addinin musulunci Wanda aka gudanar a makarantar Capital dake nan yola. Modibbo Ahmadu Kulangu yace ya kamata Al umma musulmai su kasance masu kaunan juna da Kuma amfani da kalandar addinin musulunci a dukkanin lamuransu na yau da kullum. NAFAN COLLEGE OF SCIENCE AND HEALTH TECHNOLOGY Kwalejin dake haras da kiwon lafiya kimiya da fasaha dake Unguwar Jambutu a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Kwalejin ta bude tare da fara karantar da kwasakusai a bangarorin kiwon lafiya d

Gwamnan jahar Adamawa ya shiga tsakanin domin kawo karshen ta kadda dangane da wasu kalamai da wani malami a jahar Bauchi.

Image
Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri tare da malamai addinin musulunci sunyi zaman tattaunawa domin kawo karshen cece kuce da ta faru a tsakanin malamai da malamin addinin musulunci dake jahar Bauchi Dr AbdulAziz Idris Dutsen Tanshi. Tunda farko dai gwamna Umaru Fintiri sunyi ganawar sirri da malamai da suka hada da Sheikh Abdullahi Bala Lau Sheikh Kabiru Gombe Sheik Abdulwahab Kano tare da gwamnan jahar Bauchi gwamna Bala Muhammed a gidan gwamnati daka jahar Bauchi. Da yakeyiwa manema labarai jawabi bayan fitowarsu da taron gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace sun kasance a gidan gwamnatin ne domin tattaunawa da kuma samar da masalaha dangane da furucin mallam Dr AbdulAziz Idris yayi lamarin da ya janyo martani masu zafi a fadin Najeriya. Gwamna Fintiri ya kuma yabawa gwamna Bala Muhammed na jahar Bauchi bisa kokarinsa na wanzar da zaman lafiya a fadin jahar.

Wanda ya jagorancin juyin mulki a kasar Nijar ya aiyana kasansa a matsayin shugaban kasar Nijar.

Image
A karshe dai wanda ya jagoranci juyin mulki a kasar Nijar ya aiyana kansa a matsayin shine sabon shugaban kasar Nijar. Gen. AbdulRahmane Omar Tchiani yace shine sabon shugaban kasar Nijar biyo bayab habbare gwamnatin faran hula da da dogaren fadar shugaban kasar sukayi a ranan laraba da ta gabata. Habbararren shugaban kasar Bazoum dai shine zabebben shugan na farko da ya karbi mulki a nan farar hula tunda kasar ta samu incin kanta daga kasar faransa a shekara ta 1960. Kawo yanzu dai kasashen duniya da dama suna ta tura sakonnin rashin gamsuwarsu da wannan juyin mulki da akayi a kasar Nijar. Tunin dai majalisar dinkin duniya ta sanar da dakatar da dukkanin aiyukan agaji a kasar ta Nijar kamar yadda Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ante

Majalisar dokokin jahar Adamawa ta karbi sunayen mutane 23 domin tantancesu a matsayin kwamishinoni

Image
Majalisar dokokin jahar Adamawa a ranan alami da ta ganatane dai ta karbi sunayen mutane ashirin da uku domin tantancesi domin basu mukamen kwamishinoni a jahar Adamawa. Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ne ya mikawa majalisar sunayen kwamishinoni inda gwamnan ya bukaci Yan majalisar da su tantancesu a matsayin Yan majalisar zantarwar jahar. Da yake karban sunayen kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Hon.Bathiya Wesley a yayinda ya jagoranci zaman majalisar yace zasu zasuyi maganar ranan da zasu tantance sunayen. Mutane ashirin da uku da aka mika sunayensu dai sun hada da Barr Wali Yakubu daga Madagali sai Dr John Ishaya Dabari da Mery Augustina Vasumu daga Michika sai Hon. Usman Abdullahi daga Mubi ta kudu da Tijjani Maksha daga Maiha. Dr Umar Garba Pella daga Hong. Farfesa Fintiwa David Jatau daga Gombi. Abdullahi AdamuPrambe da

Majalisar dattawar Najeriya tayi watsi da bukatan wani sanata kan sake Nmandi Kanu.

Image
Majalisar dattawar Najeriya tayi watsi da batun nan da wani sanata da ya fito daga yankin kudu masau gabas ya nemi da asako shugaban kungiyar IPOB Nmandi Kanu. Sanata mai wakiltan Imo ta yamma sanata Osita Izunaso ne dai ya gabatar da batun inda yace sakin Nmandi Kanu zai taimaka wajen kawo karshen zaman gida da yan kungiyar suka tilas tawa All ummar jahar . A Cewarsa dai tilasta zaman gidan ya gurgunta harkokin kasuwancin yankin, dama tsadar rayuwa harma da dakile tattalin arzikin yankin baki daya. Sanatocin sunki amincewa da bukatan da dan majalisar ya gabatar ne tare ta shaida masa da ya sanarwa gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kan wadannan kungiyar tare da tsare duk wanda ya karya doka. Tun a shekara ta dubu biyu da ashirin da daya ne dai wasu yan binga suka tilastawa jama a zaman gida duk da cewa kungiyar ta IPOB ta nisanta kanta daga lamarin. Yanzu haka dai shugaban kungiyar ta IPOB wato Nmandi Kanu yana tsare a yayinda

An kirayi gwamnatin jahar Adamawa da ta taimakawa manoma.....AbdulRazak

Image
An kirayi gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da tayi dukkanin abunda suka dace domin taimakawa manoma dake fadin jahar baki daya. Sarkin noman yakkire Sakin ruwan Gerio Alhaji AbdulRazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji AbdulRazak Abubakar ya yabawa gwamna Fintiri bisa na mijin kokari da yakeyi wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar harma da kokarin da yakeyi wajen tallafawa manoma dake fadin jahar. Alhaji AbdulRazak ya shawarci gwamnan dacewa in za a tallafawa manoma abi ta sarakunan gargajiya wato irin su masu angwani jimilloli hakimai Wanda acewarsa hakan zai taimaka domin sune sukasan asalin manoma dake yankunansu. AbdulRazak ya kuma baiyana cewa manoma suna taka rawan gani wajen bunkasa tattalin arziki dama rage rashin aikinyi musammanma a tsakanin matasa dake fadin jahar. Don haka akwai bukatan a maida hankali wajen taimakawa manoma aka