Mata hamsin sun samu tallafi daga shugaban darikar katolika a jahar Adamawa.
A kalla mata da mazajensu suka rasu hamsin ne suka samu tallafi kayakin abunci da kudu daga shugaban darikar katolika a jahar Adamawa. Da yake gabatar da tallafin wa matan shugaban darikar katolika a jahar Adamawa Rev. Stephen Dami Manza ya baiyana cewa ya dauki matakin rarraba kayakin ne duba da yanayi wahalar rayuwa da ake ciki a yanzu a fadin Najeriya. A cewarsa hakan yasa yayi la akari da matan da mazajensu suka rasu Wanda sunfi shiga cikin wahalar rayuwa saboda haka ya zabosu daga sassa daban daban dake fadin jahar domin ya tallafa musu Wanda haka zai taimaka wajen rage radadin wahala da suke ciki. Rev. Dami Manza ya kirayi gungiyoyi dama masu hanu da shuni da kasance sun la akari da mabukata dake cikin Al umma domin taimaka musu domin suma su samu saukin rayuwa a tsakanin Jama a . Ya Kuma shawarci wadanda suka amfana da taimakon da suyi amfani da su ta yadda suka dace domin inganta rayuwarsu Dana iyalensu harma da Samar da cigaba yadda ya kamata. Ya kirayi Yan N...