Kamfanin Dangote zai cigaba da karfafa dankon zumunci a tsakaninsa da al ummomi dake kewaye dashi.
Kamfanin Dangote ya kara jaddada a niyyar shi na na ci gaba da zaman lafiya da al'ummomi dake kewaye da shi. Babban Manajan kamfanin, Malam Bello Danmusa ne ya baiynana haka yayin zaman ganawa da masu ruwa da tsaki da ya wakana a garin Numan. Babban Manajan kamfanin, Malam Bello Danmusa yace gina kyakkyawan alaka da al'umomi dake kewaye da kamfanin abu ne wanda ya dauka da muhimmanci matuka shi yasa ma ta shirya wannan taron ganawar. Danmusa yace, kamfanin Dangote dake Numan na aiki tare da al'umomin dake kewaye da shi a fannonin ilimi da aiyukan tallafi ta hanyoyi daya tsara domin inganta rayuwan mutanen da ke yankin. A cewar shi, kamfanin Dangote zai ci gaba da ganawa da masu ruwa da tsakin domin yin hakan zai basu daman tattaunawa tare da bullo da hanyoyi da za a amfana, a kuma samu zaman lafiya tsakanin juna domin ci gaban kamfanin, al'ummomin, jaha dama kasa baki daya. Da yayi jawabi kan muhimmancin wannan zama, Babban Jami'in Ofishin hulda da al'u...