Posts

Showing posts from April, 2023

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta kama mutane tara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Image
A kokarinta na kawar da aikata taddajci a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kamar mutane tara da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa biyo bayan farmaki da ta gudanar a sassa daban daban dake fadin jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace an samu nasaran kama wadanda ake zargi ne biyo bayan baiyanai sirri da suka samu Wanda hakan yasa kwamishinan Yan sandan jahar ta Adamawa Afolabi Babatola baiyi da wasaba inda ya tura Jami an tsaro domin kamosu daga maboyansu. Rundunan karkashin jagorancin kwamandan CRACK tare da hadin gwiwar mafarauta ne dai suka kai samamen tare da nasaran cika hanu da wadanda ake zargi. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana farin cikinsu da jin dadinsa dangane da na mijin kokari da Jami an tsaro sukayi wajen kama mutane ya kuma kirayesu da su Kara himma domin ganin an magance mats...

Hukumar NAFDAC a Najeriya tasha alwashin daukan matakin daina amfani da sanadiren dake canja launin fata a fadin Najeriya.

Image
Hukumar inganta abinci da magunguna a Najeriya NAFDAC tace nan gaba kadan zata fara tilastawa na daina yi da Kuma sayar da sanadaren dake canja launin fata a fadin kasan nan baki daya Babban darektan hukumar ta kasa farfesa Mojisola Adeyeye ce ta baiyana haka a wurin taron karawa juna sani Wanda hukumar ta shiyawa yan jarida a yankin arewa masaugabas dangane da hatsarin yin amfani da sanadaren dake sauya launin fata. a Maiduguri fadar gwamnatin jahar Borno. Babbar darektar Wanda darektan sashin sanadaren hukumar Dr Leonard Omokpariola ya wakilta tace an shiyar irin wannataro wa yan jarida a jihohin Kano, Enugu, Lagos, Abuja, Jos, Ibadan, da Kuma Port Harcourt. Tace hukumar ta lura cewa yin amfani da sanadaren dake canja launin fata yana barazana da lafiyar lamarin akalla mata a Najeriya Kaso Saba in da bakwai suna amfani da sanadaren . Farfesar tace hakan yasa suka nemi hadin kana yan jarida domin su wayarwa Al umma Kai dangane da illar da yin amfani da sanadaren dake canj...

An bukaci gwamnatin tarayya dana jahar su inganta tafkin geriyo Abdulrazak.

Image
An kirayi gwamnatin tarayya dana jiha da suyi dukkanin Mai yiwa domin yashe tare da inganta tafkin geriyo domin samun cigaban dama bunkasa tattalin arzikin jahar dama kasa Baki Daya. Sarkin ruwan tafkin na geriyo Alhaji Abdulrazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a lokacin da aka nude tafkin domin kama kifi da akeyi shekara shekara a tafkin dake cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Abdulrazak Abubakar yace kama kifi da akeyi Yana taimakawa sosai harma da Samar da sana o in dogaro da Kai ga matasa. Baya ga kamin kifin ana noma abubuwa da dama a baking tafkin na geriyo Wanda Kuma hakan yana kawo cigaban da dama a bangarori daban daban. Da wannan ne yaga ya Kamata su kirayi gwamnatin da masu ruwa da tsaki da su taimaka domin kaiwa tafkin dauk duba da irin matsaloli da suke fuskanga wani lokacima ruwa tafkin kafewa yakeyi.wanda Hakan yana janyo asara masu yawa. Da yake magane dangane da kama kifin kuwa sai Abdulrazak yace bana...

An baiyana matasa dacewa suna gudumawa da zasu iya bayarwa a tsakanin al umma Sheik Duguri.

Image
An kirayi matasa da sukasance jakadu na gari a tsakanin Al umma domin sune kashin bayan kowace Al umma a fadin duniya. Sheik Ibrahim Muhammed Dugri wakilin malamai Bauchi Kuma shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala Mai shelkwata a Jos shiyar Abuja ne yayi wannan kira a ganawarsa da manem labarai a yola. Sheik Ibrahim Muhammed yace matasa suna da rawa da zasu iya takawa wajen gudanar da aiyukan cigaban Al umma don haka ya Kamata Suma su bada tasu gudumawar wajen cigaba dama wanzar da zaman lafiya. Malamin addinin musulunci ya Kuma shawarci matasan da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin Al umma Mai makon hakama kamatayayi suyi dukkanin abinda zai hada kan Jama a dama cigaban zaman lafiya yadda ya Kamata. Ya Kuma kirayi matasa da su kaucewa yin bangan siyasa sukasance masu hada kansu da girmama shuwagabanin tare dayiwa iyaye biyayya Wanda acewarta Hakan zaisa su samu Albarka a rayuwarsu a Koda yaushe. Malamin ya Kuma baiyana cewa iyaye mata Suma su...

An taya Babbar Alkalain jahar Adamawa murna rundunan yan sandan jahar Adamawa.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taya Hon. Hapsat Abdulrahman murnan kasancewarta Babban Alkalain jahar Adamawa. Rundunan ta baiyana hakane a sakon taya murna dauke da sanya hanun kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje. A sakon murnan anjiyo Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yanaceawa nada Hon. Hapsat Abdulrahman a matsayin Babban Alkalain jahar Adamawa ta cancanta kasancewarta mace ta farko da zama Babbar Alkalain a jahar Adamawa. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa ya kuma tabbatar da cewa rundunan a shirye take tayi aiki kafada da kafada domin ganin an samu nasaran yakan ta addamci a fadin jahar baki daya. Don haka kwamishinan yace a madadinsa da sauran Jami an rundunan na taya maishari a Hapsat Abdulrahman murnan samun wannan mukami na Babbar Alkalin Alkalain jahar Adamawa. A ranan talatan nan ne dai gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya tabatarwa maishari a Hapsat Abdulrahman Babbar Alkalain jahar Adamawa bayan da aka ...

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta cafke mutene biyu da aka zargi dayin garkiwa da mutane.

Rudunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran cafke mutane biyu da ake zargi masu garkiwa da mutane ne a cikin karamar hukumar Mubi ta arewa a jahar Adamawa. Kakakin rudunan yan sandan na jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace rudunan ta samu nasaran kama mutane biyu da ake zargi ne biyo bayan bayanain sirri da aka samu dangane da wadanda ake zargi. Wanda Kuma hakan yada rundunan natayi da wasaba inda ta Kai samamai tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane dake cikin karamar hukumar Mubi ta arewa a jahar Adamawa. Rundunan ta dauki matakin hakane biyo bayan rahoton da suka samu na yin garkuwa da Aisha Ahmadu da maigidanta Ahmadu Muhammed tare da kashe Mai gidannata a kauyen Digil dake ciki karamar hukumar Mubi ta arewa. Wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa da yakai nera Milyon biyu da dubu dari biyar kafin su Sako mutane. Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi...

Kungiyar manoman auduga a jahar Adamawa ta taya gwamna Fintiri murnan cin zabe.

Image
Kungiyar manoman auduga a Najeriya shiuar jahar Adamawa tana Mai Yaya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan cin zabe a matsayin gwamna jahar Adamawa a zaben gwamna da aka gudanar a wannan shekara ta 2023. Shugaban kungiyar a jahar Adamawa Alhaji Muhammed Saleh Gwalan ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Alhaji Muhammed Saleh yace a madadin kungiyar da membobinta suna taya gwamna murnan lashes zaben da shi da mataimakiyarsa Farauta. Sanarwa ta Kuma kirayi Al ummar jahar ta Adamawa ta su baiwa gwamnan hadin Kai da goyin baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar Baki Daya. Harwayau sanarwa ta taya gwamnan murnan bikin karamar sallah da fatan Allah ya karbi ibada ya Kuma maimaita mana Amin. Alhaji Saleh ya Kuma kirayi daukacin Al umma jahar Adamawa da su cigaba da yiwa jahar dama kasa adu o I samar da zaman lafiya.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tabbatar da inganta tsaro a lokacin bikin karamar Sallah.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta ce ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin inganta tsaro a lokaci dama bayan bukukuwar karamara Sallah. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahay Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanawarn na cewa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya tabbatarwa al umma jahar Adamawa cewa rundunan ta dauki kwararar matakan tsaro domin ganin an kare rayuka dama dukiyoyin al umma a lokacin bukukuwar karamar Sallah don haka al umma su gudanar da aiyukansa bisa doka su kuma kaucewa abinda zaiyiwa doka karan tsaye a lokacin bukukuwar Sallah. Kwamishinan ya kuma umurci mataimakinsa dake da aiyukan rundunan da ya tabbatar cewa angudanar da bukukuwar Sallah lafiya ba tare da matsaloliba a dukkanim yankuna dake fadin jahar ta Adamawa. Rundunan ta kuma taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Murnan dama al ummar jahar Adamawa murnan bikin karamar Sallah a wannan shekara. Kwamishinan ya kuma kira...

Munataya gwamana fintiri murnan cin zabe NULGE

Image
Kungiyar ma aikatan kananan hukumomi a Najeriya NULGE shiyar jahar Adamawa tana taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan cin zaben gwamna jahar Adamawa. Shugaban kungiyar ta NULGE a jahar Adamawa Hammajumba Gatugal ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola. Hammajumba yace a madadinsa dama membobin kungiyar dake jahar Adamawa suna masu farin cikin taya gwamnan dama mataimakiyarsa murnan nasaran lashe zabe da sukayi bayan kammala zaben gwamna da aka gudanar. Ya Kuma sahawarci daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu hada kansu da Kuma baiwa gwamnan hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa baki Daya.

Nasaran da gwmana Fintiri yayai nasarace ga al umma jahar Adamawa. Babakano jada.

Image
Alhaji Aliyu Babakano Jada yana taya gwamna Ahmadu Umaru Fnitiri murnan lashe zaben gwamna da yayi a zaben gwamna da aka gudanar a wannan shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Alhaji Babakano yace nasaran da geamna Ahmadu Umaru Fnitiri yayi nasarace ga All ummar jahar Adamawa baki daya. Don haka akwai bukatar al umma jahar su bashi hadin kai domin ganin ya gudanar da aiyukan cigaban jahar baki daya. Alhaji Aliyu ya kuma kirayi All umma jahar da sukasance masu hada kansu da kuma yin adu o i cigaba dama samar da zaman lafiya a jahar dama kasa baki daya.

Kungiyar yan jarida a jahar Adamawa ta taya gwamna Ahmadu fintiri murnan lashe zabe.

Image
Kungiyar yan jarida a Najeriya shiyar jahar Adamawa tana mai taya gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri murnan samun nasaran lashe zaben gwamna da akayi ran sha takwas ga watan hudu shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Kungiyar ta NUJ shiyar jahar Adamawa ta baiyana hakane a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hanun shugaban kungiyar a jahar Adamawa Ishaka Donald Dedan tare da sakataren kungiyar Fidelis Jocktan. Sanarwan tace a madadin dukkanin membobin kungiyar dama shugabancin kungiyar suna masu farincinkin taya gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murna yin nasaran cin zaben gwamna da aka kammala a jahar Adamawa. Na saran da Fintiri yayi ya biyo nayan irin aiyukan cigaban jahar musammanma a yankunan karkara da ma gudanar da shirye shiryen koyar da sana o i dagaro da kai da dai sauransu. Nasarawan ta kuma yaba da yadda al ummar jahar Adamawa sukuma kasance masu hakuri a koda yaushe domin samun cigaban jahar ta Adamawa baki daya. Kungiyar tana mai adu ar sabon zab...

Akalla marayu dubu daya da dari biyar ne suka samu tallafin..

Image
Kungiyar Jama atu Nasril Islam bangaren mata ta taimakawa marayu da kayaking sallah da abincin domin Suma su samu saukin gudanar da bikin sallah cikin tsanaki. Da take jawabin a wurin rarraba kayakin mataimakiyar Amiran kungiyar ta JNI a jahar Adamawa Hajiya Halima Muktar ta kurayi Al umma musulmai musammanma wadanda ke kula da marayu da su Kara maida hankali wajen kula da marayu tare da turasu makarantun addinin dana zamani domin su samu inganceccen ilimi a tsakanin Al ummah. Halima ta Kuma shawarci masu kula da marayu da daure kada sukasance masu tura talla suna gararamba a kan titi Wanda Kuma haka bazai amfanesuba. Ta Kuma kurayi iyaye da sukasance masu yiwa yaransu adu o I a Koda yaushe domin ganin sun kasance yara na gari a tsakanin Jama a. Itama anata jawabin sakatariya kungiyar ta JNI bangaren mata Hajiya Fatimatu Shuaibu ta baiyana dalilimsu na tallafawa marayu Wanda acewarta sunga ya dace marayum Suma sukasance tamkar wadanda suke da mahaifi a duniya su samu suyi wa...

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta tura jami anta domin ganin an sake zabuka lafiya.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin ganin an kammala zabe da za sake a wasu mazabu dake fadin jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace rundunan ta hada kai da takwarorinta domin daukan dukkanin matakai da suka dace domin ganin ba a samu tashin hankaliba a lokaci dama bayan zabe. Sanarwan ta kima kirayi all ummah jahar ta Adamawa da sukasance masu kai rahoton dukkanin abinda basu yarda da shiba tare kuma da baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin an kammal zaben lafiya. Harwayau sanarwa ta kara da cewa rundunan zata saka kafar wando daya da dukkanin wanda zaiyiwa doka karan tsaye. Don haka ya kamata a kaicewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al umma.

An sahawarci yan jahar Adamawa sukasanve masu hada kansu. Gwalan

Image
An shawarci Al ummar jahar Adamawa musammanma wauraren da za a sake zabe a wasu mazabu da ke fadin jahar Adamawa. da su kasance sun fito sunyi zabe cikin tsanaki ba tare da matsaloliba domin Samar da zakan lafiya da ma cigaban jahar ta Adamawa baki daya. Alhaji Muhammed Saleh Gwalan ne ya bada wannan shawarci a lokacin da ya zanta da jaridar Al Nur a yola. Fadar gwamnatim jahar Adamawa. Alhaji Muhammed Saleh yace yakamata Al ummar jahar Adamawa su sani bamu da wata jahar da ta wuce jahar Adamawa don haka akwai bukatar a hada Kai domin a gudanar da zaben lafiya. Alhaji Gwalan ya ja hankalin Al umma da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali da Kuma kada mu bari Yan siyasa suyi amfanin da mu wajen yin abinda Bai daceba a lokaci dama bayan zabe. Ya Kuma shawarci matasa da Suma su bada tasu gudumawa wajen gina kasa dama gina dumukiradiyya kasancewa sune kashin bayan Al umma don haka kar su bari ayi amfani da su wajen ta-da fitina a lokaci dama bayan zabe. Har wa...

An ja hankalin iyaye mata wajen baiwa yaransu tarbiya.

Image
Domin ganin an samu cigaban tarbiyatatar da yara an kirayu iyaye musammanma mata da sukara himma wajen baiwa yaransu tarbiya domin samun cigaban matasa a tsakanin Al umma. Mataimakiyar Amiran Kungiyar Jams atu Nasaril Islam bangaren mata Hajiya Halima Muktar ce ta bada wannan shawara a lokacin da take jawabi a wurin biking rufe tafsirin karatun Al qur ani mai girma WandaSayyida Hindu Dahiru Bauchi ta gabatar a yola. Hajiya Halima race sun dauki kwararan matakai daban daban na ganin cewa sun fadakar da mata abubuwa da yawa ta yadda zasu kula da tarbiyar yaransu dama sana o in dogaro da kai wanda acewarta daukan matakin haka zai taimaka wajen karawa matan kwarin gwiwar yiwa yaransu tarbiya. Hajiya Halima ta kara da vewa bays ga tafsirin da aka gabatar an gudanar da lacoci daban daban da zummar wayarwa matan kai dangane da yadda zasu tarbiyatar da yaransu da kuma koyon sana ar dogaro da kai.. Ta kuma kirayi al umma musulmai da su rubaiyya ibadarsu a kwanaki goma na karshen wa...

Anja hankalin Al umma musulmai wajen yin ibada a kwanaki goma na karshen Ramadan.

Image
An shawarci Al umma musulmai da suyi amfanin da wannan lokaci na kwanaki goma na karshen wata azumim Ramadan wajen rubayya ibada da adu o I domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Nakeriya Baki Daya. Shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne yayi wannan kira a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola. Alhaji Gambo Jika yace kwanaki goma na karshen watan Ramadan suna da mutukan muhimmanci ga Al umma musulmai don haka Bai Kamata ace musulmai sunyi sakaciba wajen yin adu o I da ibada. Wanda acewarsa Hakan zaitaimaka wajen samun saukin tayuwa ga Al umma Baki Daya. Alhaji Gambo ya Kuma kurayi malamai musammanma masu gudanar da tafsirin azumi da su maida hankali wajen yin was azin dukkanin abinda zai kawo hadin Kai a tsakanin Al ummah musulmai dama sauran Al umma Baki Daya. Ya Kuma shawarci Al umma musulmai da sukasance masu tausayawa juna dama taimakawa juna a Koda yaushe domin samun cigaban addinin m...

Wani dan shekaru saba in da haifuwa. ya shiga komar yan sanda bisa zarginsa da yin fyade a jahar Adamawa.

Image
Rundunan yan sandan jajar Adamawa ta cika hanu da wani mutum dan shekaru saba in da haifuwa bisa zargginsa da yiwa wasu kananan yara biyu fyade a jahar ta Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a yola. Sanarwan tace mutumin mai suna Usman Ibrahim ya shiga koman yan sandan ne biyo bayan rahoton da uban yaran ya kai ofishin yan sandan dake Jimeta a cikin karamar hukumar yola ta arewa. Wanda hakan yasa Jami an yan sandan basuyi da wasaba wajen damko wanda ake zargin. Sanarwan ta cigaba da cewa ana zargin mutuminne da yaudaran yaran zuwa daki a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa karatun saboda haka sai yayi amfani da wannan damar. Kawo yanzu dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiwa sahin binciken manyan laifuka wato CID damar gudanar da bincike kan lamarin. A binciken farko da aka gudanar dai an gano cewa mutumin yana yara uku kuma...

Gidauniyar Attarahum ta taimaka da kayakin Azumi a jahar Adamawa.

Image
Gidauniyar Attarahum ta taimakawa marassa galihu da kayakin Azumi domin su samu saukin rayuwa atsakanin al umma a wannan lokaci na azumin watan Ramadan. Gidauniyar tayi wannan taimakonne a yola ga wadanda suka fito daga sassa daban daban daga ciki da wajen fadar gwamnatin jahar Adamawa. Da yake jawabi a lokacin rabon kayan shugaban Gidauniyar ta Attarahum a jahar Adamawa Mallam Muktar Dayyib yace sun dauki matakin wannan taimakonne duba da yanayi da yanayi da ake ciki na azumi domin neman yardan Allah madaukakin sarki tare da samun lada mai yawa. Mallam Muktar yace ankafa gidauniyar Attarum ne domin taimakon kai da kai don haka nema suka ga ya dace su fadada taimakon zuwa ga al ummah daban daban. Mallam Muktar ya kuma kirayi kungiyoyi dama masu hanu da shuni sukasance masu taimakawa marassa galihu a koda yaushe domin samun cigaba yadda ya kamata. Ya kuma jaddada aniyar gidauniyar na cigaba da taimakawa al umma a koda yaushe domin ganin al umma sun samu saukin rayuwa yadda y...