Manoma da makiyaya an bukacesu da su rungumin zaman lafiya a tsakaninsu.
A wani mataki na kawo kashen ta kaddama a tsakanin makiyaya da manoma fadin Najeriya an shawarcesu da sukasance masu hada kansu da fahintar juna a tsakaninsu domin wanzar da zaman lafiya Mai daurewa da Kuma cigaban aiyukansu yadda ya kamata. Kwamnadan Mafarauta na kasa Kuma Sarkin yakin mafarauta Adamawa Alhaji Muhammed Adamu ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola. Alhaji Muhammed Adamu yace ya kamata manoma da makiyaya su sani cewa su Yan uwan junanne kar su bari shaidan ya shiga tsakaninsu, sukasance masu taimakawa juna da yarda da juna a Koda yaushe domin ganin ba a samu tashin hankali a tsakaninsuba. Alhaji Adamu yace rikici a tsakanin manoma da makiyaya ba karamin koma baya bane musammanma a bangaren tattalin arziki da asaran rayuka dama dukiyoyi masu yawa. Acewarsa dai ya kamata manoma da makiyaya su kaucewa duk abinda zai kawo tashin taahina a tsakaninsu su rungumi zaman lafiya da taimakawa juna domin samun cigaba. Ya Kuma shawar...