RUNDUNAN YAN SANDA JAHAR ADAMAWA TA KAMA MUTANE BIYU DA AKE ZARGI YAN FASHI DA MAKAMI.

A gudanar da aiyukanta rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta sake yin nasaran a kokarinta na yaki da aikata laifuka yayi nasaran cika hanu da mutane biyu da ake zargin Yan fashi da makami ne tare da gano mota da aka sace. Kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Hayaha Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema a Yola. Biyo bayan samun bayanain sirri offishin rundunan Yan sandan dake yolde pate karkaahin jagorancin SP Abdullahi Abubakar basuyi kasa a gwiwaba inda suka Kai daukin gaggawa biyo bayan samun labarin anyiwa Wani Mai suna Umar Sani fashi tare da kwace masa motarsa Kiran Honda na shekara ta 2015 a sabon gari Jalingo dake jahar Taraba inda aka tafo da ita zuwan Nan Yola. Wadanda ake zargin dai sun hada da :Emmanuel Sale (Mai shekaru 28 da haifuwa).2.Jibrilla Hassan ( Mai shekaru 36 da haifuwa).Dukkaninsu mazaunan sabon gari Jalingo ne an kamasu tare da gano motar da sata. Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa CP Dankwambo Morris,psc(+), ya yab...