Ambaliya: An shawarci Al umma daina tushe magudanain ruwa.
A wani mataki na inganta harkokin noma da Kuma kaucewa ambaliyar ruwa an kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai dama masu ruwa da tsaki da Al umma da sukasance masu aiki kafada da kafada domin magance matsalar baki Daya. Kwamandan Mafarauta na kasa Kuma Sarkin yakin mafarautar jahar Adamawa Alhaji Muhammed Adamu ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai dangane da harkokin noma dama ambaliya. Alhaji Muhammed Adamu yace yana da muhimmanci gwamnatin tarayya Dana jihohi har da na kananan hukumomi da su Kara himma wajen yiwa Al umma ingantattun mugadanen ruwa Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen kariya daga ambaliyar ruwa, dake janyo asarar masu yawa da suka hada dana rayuka da dukiyoyi da dai sauransu. Alhaji Muhammed ya Kuma shawarci Al umma da su guji zuba shara a magudanen ruwa Mai makon hakama sukasance masu tsafcace mugudanen ruwa domin toshe mugudanen ruwa shine yake sanadiyar ambaliyar ruwa don haka jama a su guji toshe magudanen ruwa. Alhaji Muhammed Adamu ya ya bai...