Posts

Showing posts from August, 2023

An bukaci masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin samarwa manoma sauki.

Image
An kirayi masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin ganin an samu rangwame a bangaren maifetur saboda samarwa manoma saukin gudanar da harkokinsu tadda ya kamata. Shugaban kungiyar manoma Yakkore dake Jambutu Alhaji AbdulRazak Abubakar ne ya wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji AbdulRazaka yace tsadar maifetur yana gurgunta aiyukan noma sosai saboda haka ya zama wajibi su kirayi masu ruwa da tsaki da su taimaka su shiga tsakanin domin warware matsalolin baki daya. AbdulRazak ya Kara dacewa manoma a jahar Adamawa musammanma kananan manoma suna fuskantar kalubale da dama da suka hada da rashin taki, magungunan feshi, da dai sauransu, wanda kuma acewarsa hakan na haifar da koma baya a bangaren noma. Da wannan ne yake kira ga gwamnatin tarayya dana jahar da suyi dukkanin abunda suka dace domin ganin manoma sun samu saukin gudanar da ai...

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta samu nasaran kama matasa hudu da ake zargi da dayin amfani da yanan gizo domin sace kudaden Jama a.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kama wasu matasa hudu dake amfani da yanan gizo wajen kwashewa Jama a kudadensu daga asusun ajiyarsu dake Bankuna. Sashin binciken manayan laifuka na rundunan wati CID ne sukayi nasaran kama matasa wadanda dukkaninsu suna zaune ne a Anguwar Shagari rukunin na biyu dake cikin karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa. Kakakin r rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola. Sanarwan ta baiyana cewa kawo yanzu dai bincike ya nuna cewa wadanda ake zaigi suna aikata lafin haka tun daga shekara ta 2022. Da wannan ne kwamishinan dan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yasha alwashin dakile duk wasu laifuka a fadin jahar, kuma yace da zaran an kammala bincike kan wadanda ake zargi za a gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shariya. Ya kuma kirayi al umma da su taimak...

Gidauniyar Attarahum ta bukaci hadin kan kafafen yada labarai wajen gudanar da aiyukansu.

Image
Gidauniyar Attarahum ya nemi hadin Kai kafafen yada labarai dake fadin jahar domin ganin sun cimma burinsu na taimakawa Al umma dake fadin jahar baki daya. Shugaban Gidauniyar ta Attarahum a jahar Adamawa Mallam Mukhatar Dayyib ne ya baiyana haka a lokacinda suke ziyarata kafafen yada labarai dake nan yola. Mallam Mukhatar Dayyib yace Gidauniyar ta Attarum Yana maida hankali wajen taimakawa marassa galihu, marayu dama sauran mabukata. Yace sun dauki matakin ziyarta kafafen yada labarain ne domin neman goyon bayansu domin ganin sun samu nasaran gudanar da aiyukansu na taimakawa jama a. Malam Dayyib ya Kuma baiyana cewa Gidauniyar na da rassa a dukkanin kananan hukumomi ashirin da Daya dake fadin jahat ta Adamawa harma da anguwanin dake cikin kananan hukumomin. Don haka Gidauniya na tsaye daram domin ganin an taimakawa Al umma dake cikin da wajen jahar t...

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta raba Jami anta biyu da aikinsu.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ya raba Jami an yan sanda biyu da aikinsu biyo bayan samunsu da lafin kisan Kai. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola. Jami an yan sanda da lamarin ya shafa dai sun hada da Ahmed Suleiman Mai mukamin isfeta, da Mahmood Muhammed Mai mukamin kostabul Kuma dukkaninsu suna aikine a ofishin rundunan dake Dumne dake cikin karamar hukumar Song a jahar Adamawa. Biyo bayan bincike da rundunan ta gabatar ya samu Jami an da lafin kisan Kai don haka an Koresu da aiki kamar yadda dokan rundunan Yan sandan na sashi 370 Wanda akayiwa gyara a shekara ta 2020 na cewa duk Jami in Dan sanda da aka samu da lafin kisa za a hukuntashi tare da koransa daga aikin Dan sanda. Saboda haka bayan an Koresu za a gurfanar dasu gaban kotu domin su ...

An bukaci baiwa gwamnati da kwamitin rarraba kayakin tallafi hadin Kai a jahar Adamawa.

Image
jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintir ta kudiri aniyar taimakawa al ummar jahar domin rage radadin wahala da ake ciki biyo bayan cire tallafin mai fetur wanda gwamnatin tarayya tayi. Mai taimakawa gwamna fintiri na musamman kan harkokin jama a Barista Sunday Wugira ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a yola. Barista Sunday yace tuninma aka sayar da taki da yakai tirela ashirin cikin farashi mai rafusa ga manoma dake fadin jahar. Wanda kuma an dauki matakin hakane domin bunkasa harkokin noma a fadin jahar domin samun saukin kayakin abinci a fadin jahar. Barista Wugira yace da yardan Allah nan gaba kadan za a kawo tirelar masara hamsi dana shinkafa ashirin domin ganin an samawa al ummar jahar saukin rayuwa da kuma rage radadin kuncin rayuwa da al ummar suka tsinci kansu a ciki. Barista ya kuma baiyana cewa a b...

An shawarci gwamnatin tarayya Dana jihohi da su Kara kaimi wajen dakile rikici a tsakanin manoma da makiyaya.

Image
An kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da su kara kaimi wajen daukan matakin kawo karshen rikici a tsakanin makiyaya da manoma a fadin Najeriya baki daya. Shugaban kungiyar Sullubawa ta kasa shiyar jahar Adamawa Alhaji Bello Ardo ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji Bello Ardo ya yabawa gwamnatin tarayya dana jihohi bisa kokari da sukeyi na warware matsaloli dake faruwa a tsakanin manoma da makiyaya a fadin Kasan nan don haka akwai bukatar su kara himma wajen dakile matslar baki daya. Don farfado da tattalun arzikin, samar da zaman lafiya cigaban a jahar dama kasa baki daya. Ya kuma kirayi hwamnatin tarayya dana jihohin da cewa in har zaau kafa kwamiti dangane da abinda ya shafi manoma da makiyaya to ya kamata su hada da shuwagabanin makiyaya dana manoma wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen kawar da rikici...

Kasar Jamus zata taimakawa karamar hukumar Michika dake jahar Adamawa.

Image
Karamar hukumar Michika tana Daya daga cikin kananan hukumomi da ta fuskanci rikin boka Haram a yankin Arewacin jahar Adamawa. Karamar hukumar Michika dai tanadaga cikin kanan hukumomi suke gudanar da harkokin noma kiwo dama kasauwanci daban daban, mata da dama a karamar hukumar ta Michika suna gudanar da harkokin noma dama kasuwanci daban daban. Hakan yasa gwamnatin kasar Jamus ta kudiri aniyar taimakawa karamar hukumar domin tada komadan tattalin arziki da ta samu sakamokon matsalar tsaro. A wurin bikin kaddamar da bada taimakon da za ayiwa angwani goma sha shida dake karamar hukumar ta Michika a jahar Adamawa. Darectan GIZ a Najeriya Da ECOWAS Dr Markus Wagner tare da farkon sakatare ofishin jakadancin Jamus a Najeriya dake Abuja Susane Schroder sukace Samar da wadaceccen abinci da tallafawa zai taimaka wajen cigaban yankin yadda ya kamata. Shi...

Rundunan bada kariya ga fararen hula Civil Defence Tasha Alwashin inganta tsaro a jahar Adamawa.

Image
A kokarinta na dakile aiyukan ta addanci da aikata laifuka a tsakanin al umma dama kare kayakin jama a da dukiyoyi harma da rayukan al umma dake fadin jahar Adamawa. Rundunan tsaro kare fararen hula a Najeriya wato NSCDC shiyar jahar Adamawa ta kama mutane biyu da ake zargi da fasa runbun Adana kayakin gona dake kusa da mayanka a hanyar Yola. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa wanda mai magana da yawun rundunan a jahar Adamawa SC Dimas Yakubu Bille ya sanyawa hanu kuma aka rabawa manema labarau a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Sanarwan ta baiyana cewa ma aikatar muhalli dake jahar Adamawa tana iya kokarinta wajen inganta muhalli wanda hakan yana taimakawa wajen gudanar da harkokin noma yadda ya kamata, a fadin jahar. Wadanda aka kama dai sun hada da Ibrahim Abdullahi da Yusuf Muhammed harwayau rundunan tana cigaba da tsare wasu m...

An baiyana cewa hanyoyin sadarwa suna da muhimmanci a bangaren jinkai.

Image
Inganta harkokin sadarwa ne Ka dai zaitaimaka wajen bada agajin gaggawa ta yin amfani da kafafen yada labarai. Manajan aiyuka na BBC media action Nicolas Raul ne ya baiyana haka a lokacin kammala horo da akayiwa kafafen yada labarai da masu aiyukan jinkai a jahar Adamawa Nicolas Raul yace sama da shekaru ashirin bbc media action tana aiyukan taimakawa mutane da suke da bukatar agaji biyo bayan hali da suka shiga sakamokon rikici. Ya Kuma kara da cewa sadarwa yana taka muhimmiyar rawa wajen aiyukan jinkai don haka ne ma suka shiryawa kafafen yada labarai da masu aiyukan jinkai wadanda suka fito daga jihohi Adamawa da Borno hora na musamman domin samun cigaba Wanda ya jagoranci horaswa na BBC media action Deji Arosho da Sumayya Ibrahim Yusuf sun gabatar da kasidu masu taken akwai bukatar inganta sahin sadarwa domin sadarwa Yana daga cikin aiyukan jinkai Sun Kuma baiyana...

Gwamnatin jahar Gombe ta bada umurnin rufe dukkanin gadajen rawa dake fadin jahar.

Image
Gwamnan jahar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bada umurni da a gaggauta rufe dukkanin gidajen rawa dake fadain jahar. Sakataren gwamnatin jahar Gombe Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya sanar da haka inda yace an dauki matakin hakane biyo bayan korefe korofe da jama a keyi dangane da gidajen na cewa ana samun tabarnarewar tarbiya, aikata laifi, harma da matsalar tsaro. Gwamnan ya kuma umurci rundunan tsaro bada kariya ga fararhula wato Civil Defence kakashin Operetin Hattara da su tabbatar abin wannan umurni a fadin jahar baki daya. Gidajen rawa da suka shafa dai sun hada da Jami a gidan wanka dake mil uku akan hayar Yola,, a Gimbe, da white House Theatre, (Babban Gida), wanda yake sabon titin zuwa Yola a mil uku,sai gidan lokaci General merchant da dai sauransu.

Rundunan yan sandan jahar Bauchi ta damke wani makayayi da ake zargi da sare hanun manomi.

Image
Rundunan yan sanda a jahar Bauchi ta samu nasaran cafke wani Mai suna Adamau Ibrahim Dan shekara sha biyar da haifuwa Wanda ke kauyen Jital akan hanyar da ta hada Jihar Gombe da Bauchi.bisa zarginsa da sare hanun wani manomi. Kakakin rundunan yan sandan na jahar Bauchi SP Ahmed Muhammed Wakil ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a jahar Bauchi. A binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa sau da dama Wanda ake zargin Yana shiga gonar Wanda aka jiwa raunin da shanunsa. Lamarida yasa Mai gonar ya Kai kukansa ga baban Wanda ake zargi inda ya shaida masa cewa ya shiga gonarsa da dabbibi Kuma amsa barna sosai a gonar. Harwayau bincike ya nuna cewa a ranan 24-8+2023. Wanda ake zargin dauke da sanda da Kuma addarsa ya kusa gonar tare da lalata amfanin gonar. Biyo bayan haka ne Mai gonar ya umurceshi da ya fita daga gonarsa, sakamokon hakane Wanda ake zargin ya zare ad...

Hukumar dake yaki da fataucin mutane tayi gargadi da a lura da masu safaran mutane a jahar Adamawa.

Image
Hukamar dake yaki da safaran mutane ta kasa NAPTIP shiyar jahar Adamawa ta gargadi mazauna jahar Adamawa da sukasance masu sanya idi da Kuma maida hankali wajen aiyuka masu safaran mutane a Koda yaushe. Shugaban hukumar ta NAPTIP a jahar Adamawa Malam Adamu Ibrahim Bah ne yayi wannan gargadi a zantawarsa da manema labarai a yola. Shugaban yace hukumar yanayin dukkanin abinda zata iya domin tabbatar da ganin an dakile aiyukan masu safaran mutane a fadin jahar baki daya. A cewarsa dai yanzu hakama hukumar ta fara gangamin wayarwa Al umma Kai dangane da matsalar ta safaran mutane a wurare daban daban da suka hada da masallatai, makami u da dai sauransu. Ya Kuma baiyana cewa gwamnati na iya kikarinta na ganin an dakile aiyukan safaran mutane a fadin Najeriya Harwayau shugaban hukumar Malam Adamu yace hukumar ta NAPTIP zata hada Kai da sauran hukumomin tsaro wajen yin aiki tare a wani mataki na kawar da aiyukan ...

Gwamnatin jahar Gombe ta lashi takwabin bunkasa harkokin kasuwanci a jahar.

Image
Gwamnanatin jahar Gombe ta lashi takwabin ganin an bunkasa harkokin kasuwanci domin amfanar al ummar jahar baki daya. Gwamnan jahar ta Gombe Muhammed Inuwa Yahaya ne ya bauyana haka a lokacinda ya marabci tawagan kamfanin Lafarge Africa PLC.a ziyaran da suka kai masa. Tawagan karkashin jagorancin group managing darecta kamfanin Mr Lolu Alade tare da managing darectan kamfanin simitin Ashaka da dai sauransu ne suka kaiwa gwamnan ziyara. A tattaunawa da sukayi dai sun tsaida shawaran hada karfi da karfe domin hada kai da gwamnatin jahar Gombe da kamfanin siminti domin ganin an samu cigaba a fannoni daban daban a fadin jahar baki daya. Taron tattaunawar ya samu halartan sakataren gwamnatin jahar ta Gombe Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi tare da kwamishinan ciniki a jahar Barista Zubair Muhammed Umar kuma ciroman Gombe.

Kwamiti rarraba kayakin tallafi na jahar Gombe ya kaddamar da fara rarraba kayakin tallafi a jahar Gombe

Image
Kwamitin rarraba kayakin tallafi a jahar Gombe biyo bayan matsanancin tattalim arziki da aka shiga bayan cire tallafin maifetur da gwamnatin tarayya tati. Ya kaddamar da fara rarraba tallafin kayakin abinci da sauransu a cikin karamar hukumar Kwami dake jahar ta Gombe. Gwamnan jahar ta Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya jagorancin kaddamar da fara rabon kayakin a karamara hukumar ta Kwami. Gwamnan wanda mataimakinsa Manassah Jatau ya wakilta yace gwamnatinsa zatayi dukkanin maiyiwa domin fadada aiyukanta wajen taimakon Al ummar dake fadin jahar baki daya. Gwamnan yace wahalar da jama a suka shiga sakamokon cire tallafin maifetur yayi sanadiyar samarwa jama a damuwa sosai don hakane gwamnati taga ya dace ta tallafa domin ganin al umma sun samu saukin rayuwa. Ya kuma kirayi al umma musammanma matasa da su rungumi harkokin noma dama koyon sana o i dogaro da kai wanda acewarsa haka zaitaimaka wajen rage radadin wahala da ake ...

Gwamnan jahar Gombe ya amince da nadin sakataren da na musamman.

Image
Gwamnan jahar Gombe Muhammed Inuwa Yahaya ya amice da nada Mohammed Usman Shanu a matsayin sakatarensa na musaman. Muhammed Ahmed Shaunu ya maye gurbin tsohon sakataren Ahmed Kasimu Abdullahi wanda kawo yanzu an nadashi a matsayin shugaban ma aikatan jahar na riko tun a watan mayun wanan nan shekara. Kafin nadashi a matsayin sakatare na musamman Muhammed Shanu shine Babban darektan aiyuka a ofishin sakateren gwamnatin jahar ta Gombe. Gwamnan kuma ya amice da Alhaji Ahmed Kasimu Abdullahi a matsayin shugaban ma aikatan jahar na riko kuma zai fara aikne a nan take.

Shugaban kasar baice komaiba dangane da hatasari jirgin Saman da yayi sanadiyar mutuwar shugaban sojojin Wagner.

Image
Kawo yanzu dai shugaban kasan Rasha Vladimir Putin baice komaiba dangane da hatsarin da jirgin sama dake dauke da shugaban sojojin Wagner yayi a kasar ta Rasha. Shugaban na Rasha yace shugaban sojojin Wagner mutunin da ya tafka kurakure a rayuwarsa. Shugaba Putin tunin ya ake da ta aziyarsa ga iyalen mutane goma dake cikin jirgin wanda yayi hatsari a yammacin ranan laraba a Moscow. Yanzu haka dai gwamnatin kasar ta Rasha tace zata gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin.

An baiyana cewa shayar da jarirai nonon uwa Yana da mutukan muhimmanci. Malama Jummai

Image
An shawarci iyaye mata musammanma masu shayarwa da su maida hankali wajen baiwa jariransu mama Akai akai domin ganin sun samu cikekken lafiya da Kuma kuzari a Koda yaushe. Malama Jummai Wycliffe kwararriya a fannin mata masu dauke da Juna biyu da Kuma shayarwa a asibitin kwararru dake yola, ne ta bada wannan shawara a zantawarta da Jarida Al Nur Hausa dangane da watan shayar da jarirai nonin uwa ta duniya. Malama Jummai tace shayar da jarirai nonon uwa Yana da tasiri sosai domin Yana baiwa jarirai kariya daga cututtuka daban daban, ga koshin lafiya, da Kuma Kara son Juna a tsakanin uwa da jarirai. Da wannan nema ta kirayi magudanta da sukasance suna baiwa mata masu shayarwa kula sosai da karamusu kwarin gwiwa wajen shayar da jarirai yadda ya kamata. Ta Kuma shawarci mazaje da sukasance suna baiwa mata musammanma wadanda ke dauke da Juna biyu kyakkawa...

An zargin wani Dan shekaru casa in da hudu dayiwa yar shekaru sha uku da haifuwa fyade a jahar Adamawa.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta cika hanu da wani mutum mai shekaru casa in da hudu da haifuwa yayiwa yar shekara sha uku da haifuwa fyade a cikin karamar hukumar Ganye dake jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Sanarwar ta baiyana cewa mutumin mai suna Muhammadu Abubakar dan shekara casa in da hudu yana zaune ne a unguwar Tappare dake cikin karamar hukumar ta Ganye. Wanda kuma yana aiyana kansa dacewa mai maganin gargajiyane, inda yake yaudaran yaran mata dacewa zai baau minti da dai sauransu. Inda yake amfani da wannan damar wajen cin zarafinsu. Bincike ya nuna cewa an kama wanda ake zargine biyo bayan raunin da yarinyar taji wanda hakan yasa mamanta ta tambayeta ina ta samu wannan rauni bayan ta gayawa mamannatane sai ta garzaya ofishin yan sanda dake Ganye...

An rantsar da kwamitin da zai gudanar da rabon tallafi wa jama a domin rage radadin wahala sakamokon cire tallafin maifetur

Image
Gwamnan Jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya bukaci mambobin komitin tsarawa da rabon tallafi na jaha da su guji son kai yayin gudanar da aikin da aka daura musu. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya mika wannan bukata ne a ranar laraba yayin kaddamar da komitin rabon tallafin mai mabobi 22 wanda aka yi a dakin taro dake gidan gwamnati a birnin yola. Gwamna Fintiri wanda mataimakiyar shi, farfesa Kaletapwa George Faruta ta wakilta yayin kaddamar wan yace al’ummar jahar Adamawa na fama da wahalhalu sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin taraiya ta yi, inda gwamnatin jahar ta yanke shawarar bullo da wasu matakai da za su taimaka gurin rage radadin, hakan ya sa ake bukatan komiti wanda babu son kai ko ma wani iri ne. Gwamnan yace an daura wa komitin hakkkin bullo da dukkan dabaru da ake bukata na zirga zirgan kayakin tallafin daga ma’ajiya zuwa inda za a gudanar da rabon, da kuma sa ido tare d...

A yau ne gwamnan jahar Adamawa zai rantsar da kwamitin rabon tallafi

Image
Gwamnatin jahar Adamawa tace zata rantsar da komitin raba tallafi a yau laraba 22 ga wata sabanin ranar alhamis 23 ga watan agusta da ta sanar a can baya. Za a kuma yi bukin kaddamarwan ne a dakin taro dake gidan gwamnati a birnin Yola. Sauyin ranar dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarun gwamna, Humwashi wonosikou ya aike wa manema labaru. sanarwan ta kuma umurci Komitin rabon tallafin wanda ya kunshi mutum 20 karkashin shugaban cin sakataren gwamnatin jaha, Auwal Tukur da su hallaru da karfe tara da rabi na safiya. Gwamnan jaha Ahmadu Umaru Fintiri ya kuma bada umirnin cewa mambobin komitin su tabbatar da adalci yayin rabon tallafin tare da la'akari da manufar gwamnati na kula da jin dadin yan jahar. Har wayau a ranar laraban za a rantsar da sabon mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labaru, Baba Yola Toungo da zaran an kammala r...

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tana tsare da mtane biyu bisa zarginsi da garkuwa da mutane.

Image
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta baiyana cewa mutane biyu sun shiga Jakarta biyon zarginsu da yunkurin yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa. Kakakin runduna yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da aikewa manema labarai a yola. Sanarwan tace an samu nasaran kama wadanda ake zarginne biyo bayan yadda suka kira wadansu mutane biyu wato Halilu Bello da Abubakar Hammanyaro harda yi musu barazana cewa subiya milyon gima ko su akasu lahira. To sai dai hakarsu bata cimma ruwan don kuwa yanzu haka suna hanun yan sanda domin cigaba da bincike. Wadanda ake zargin dai sun hada da Abdullahi iIya dan shekara ashirin da haifuwa, da Barkindo Yahaya shi kuma shekarunsa sha Tara ne da haifuwa, dukaninsu dai mazauna garin Kojoli ne dake cikin karamar hukumar Jada a jahar Adamawa.

An kirayi Shuwagabani da sukasance masu adalci.

Image
An kirayi shuwagabani a dukkanin matakai da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa adalci da gaskiya da rikon amana domin samun tsira ranan gobe kiyama. Sanannen malamin addinin musuluncin nan Sheirk Dr Sani Rijiyar Lemo ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin taron kwamitin Da awa na mata ta kasa da aka gudanar a jahar Gombe. Sheirk Sani Rijiyar Lemo yace ya kamata shuwagabani sukasance masu sanya tsaron Allah Madakakin sarki a zukatansu domin ganin sunyi adalci a ahugabancinsu. Da take jawabi a wurin taron uwar gidan mataimakin ahugaban kasa Hajiya Nana Kashim Shettima wanda uwar gidan gwamnan jahar Borno Hajiya Falmata Babagana Zulum ta wakilta ta baiyana cewa mata sune na gaba gaba wajen yiwa yara tarbiya na gari. Ta kuma kirayi kwamitin mata masu Da awa da su hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu domin magance matsalar shaye sha...