Rundunan yan sandan Najeriya ta lashi takwabin kama duk Wanda yake da hanu a kisan Jami anta shida a jahar Delta.
Rundunan yan sandan Najeriya tace yanzu haka ta tsumduma cikin gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hanu a kisan Jami an yan sanda a wani hatsaniya da ya faru a Ughelli dake jahar Delta. Lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Jami an Yan sanda shida inda harziwa yanzu a Kai ga gano Yan sanda shida ba. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da maimagan da yawun rundunan ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja. Biyo bayan kwararar bin cike da aka gudanar yanzu haka ana tsare da mutane takwas da ake zargi da hanu a cikin harin kwanyan bauna da akayiwa Jami an Yan sandan, tun da farko dai an kama mutane biyar, kana daga bisani an kama mutane uku a wurare daban daban. Biyo bayan hadin Kai da aka baiwa rundunan ne ya bada samun nasaran kama wadanda ake zargin Wanda jimlansu yaka takwas. Wadanda aka kama suna tsare a hanun Yan sanda Kuma suna taimakawa wajen gudanar da bincike . Kuma runduna Yan sandan a shirye take ta kama duk wadanda suke da hanu a cikin lamarin Kuma da zaran...