Kungiyar NASWDEN Shiyar karamar hukumar yola ta Arewa ta rantsar da sabbin shuwagabanninta a jahar Adamawa.
An kirayi shuwagabanin masu sana ar kayakin Bola a jahar Adamawa da su kasance masu gudanar da shugabancin su bilhakki da gaskiya domin ganin an samu cigaban kungiyar yadda ya kamata a fadin jahar ta Adamawa. Shugaban dattawan kungiyar masu sana ar kayakin Bola a jahar Adamawa Alhaji Aiwalu Bashiru ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bikin rantsar da shuwagabanin kungiyar na shiryar karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Auwal Bashiru yaja hankalin shuwagabanin da su maida hankali wajen kare martabar kungiyar a idon Al umma da Kuma gudanar da aiyukan cigaban kungiyar dama tsafcaceta domin ganin an daina kallon kungiyar da mamunan zato. Haka kazalika ya kirayi kwamitin cika aikin kungiyar da su Kara hazaka domin zakulo dukkanin masu yiwa kungiyar zagon kasa ko natawa kungiyar suna domin Yi musu hukunci. Domin acewarsa akwai wasu dake gudanar da aiyukansu ba bisa Ka idaba da sunan kungiyar. ...