Bunkasa Noma: mata hamsin sun samu tallafi kan noma daga kamfanin Dangote a jahar Adamawa.
Kamfanin Dangote dake Numan ta kaddamar da shirin tallafin Naira miliyan biyu da rabi wa mata manoma da dake ƙauyukan da ke kewaye da ita. A jawabin shi yayin bukin kaddamar wan da ya wakana a harabar kamfanin, gwamnan jahar Adamawa Umaru Fintiri ya gode wa kamfanin da yadda ya yunkura domin saka mata cikin shirye shiryen ya na bada tallafi. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya samu wakilcin Komishiniyar Ma'aikatar harkokin mata Neido Geoffrey Kofulto yace mata suna da jajircewa da sa kai a dukkan abun da aka saka su, shi yasa kamfanin Dangote ya ba su wannan dama domin tallafa musu. Gwamnan ya shawarci matan da suyi amfani da wannan kudin ta hanyar da aka tsara su saboda a samu sakamakon da zai kara bude kofa domin wasu ƙarin matan su ma su amfana. Fintiri ya godewa sarakunan gargajiyan yankin da yadda suke baiwa Kamfanin goyon bayan tafiyar da ayyukan ta da ma sauran shirye shirye wa mutanen su. A nashi jawabi, daya daga cikin manyan jagororin kamfanin Dangote...