Babban Hafsan tsaron Najeriya ya gana da Babban sifeton yan sandan Najeriya.
A wani mataki na inganta tsaro da kuma hadin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro, Babban Hafsan tsaron Najeriya janaral Christopha Gwabin Musa tare da manyan Jami an soji sun ziyarci Babban sifeton yan sandan Najeriya a ofishinsa dake shelkwatar rundunan a Abuja domin kara karfafa halaka da kuma hada kai wajen yin aiki tare a tsakanin yan sandan da sojoji domin kare kasa daga matsalar tsaro. Kakakin rundunan yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar wanda kuma aka rabawa manema labarai a Abuja. Babban Hafsan tsaron ya taya Babban sifeton yan sandan murnan tabbatar da nadinsa a matsayin Babban sifeton yan sandan Najeriya tare yaba masa bisa kokarinsa na tura rundunan yan sandan kwantar da tarzoma domin dakile aiyukan masu tada kayan baya. Tare kuma da nuna alhininsa da harin da wasu sojoji suka kai a shelkwatan rundunan yan ...