Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta shiyar B tace tayi nasaran kama mutane akalla dari tara da saba in da bakwai a shekara ta 2022.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya N D L E A shiyar B Wanda ya kunshi jihohi Adamawa, Taraba da kuma jahar Gombe tace tayi nasaran kama mutane dari Tara da saba in da bakwai wadanda ake zargi da safaran miyagun kwayoyi a Yankin na B. Kwamadan hukumar a yankin na B Alhaji Idris Bello ne ya baiyana haka a lokacin da yake Zantawa da jaridar Al Nur a yola, dangane da irin nasarorinda hukumar ta N D L E A tayi a shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu a yankin. Kwamandan yace cikin wadanda aka kama dari tara da saba in da bakwai wadanda suka hada da mata an yankewa dari uku da sittin da biyar hukunci a yayinda dari uku da saba in da hudu kuma an basu shawarwari domin su daina ta ammali da miyagun kwayoyin. Alhaji Idris Bello ya kuma baiyana cewa hukumar tayi nasaran kama miyagun kwayoyi da nauyinsa yakai kilo grama milyon biyu da dubu dari bakwai da hamsin da bakwai da dari tara da saba in da uku. Wato 2,757,973. Da wannan ne kwamandan...