An shawarci Al umma da bunkasa harkokin Al adu domin Samar da hadin Kai a tsakanin Al umma.
. An shawarci al umma da su maida hankali wajen kula dama bunkasa harkokin al adu domin samun hadin kai harma da wanzar da zaman lafiya a tsakanin Jama a. Shugaban kungiya baoys brigade a Najeriya shiyar karamar hukumar Girei a jahar Adamawa Mr Joshua Philemon ne ya bada wannan ahawara alokacinda yake jawabi a wurin bikin rawai rawain gargajiya da kungiyar ta shirya a Karamar hukumar ta Gieri a jahar Adamawa. Mr Joshua Philemon yace makasudin shirya wannan biki shine domin musayar fasaha da da a a tsakanin membobin kungiyar ta Boys brigade da kuma samun damar koyon Al adu daban daban domin samar da cigaba yadda ya kamata. Ya kuma jaddada cewa koyon Al adu daga Al ummomi daban daban zai takarawan gani wajen kare Al adu dama infanta rayuwar Al umma baki daya. Ya kuma kirayi membobin kungiyar da sukasance masu bin doka da oda a koda yaushe domin samar da inganceccen tsaro harma da cigaba. A jawabinsa uban kungiyar ta boys brig...