Wasu da ake zargi Yan fashi da makamine sun shiga hanun Yan sanda a jahar Adamawa.
A kokarinta na yakan masu aikata laifuka rundunan yan sandan jahar Adamawa ta cafke mutane biyu da ake zargi da kitsa da Kuma yin fashi da makami. Wadanda ake zargin dai sun hada da Umar Faruk Dan shekaru 25 mazaunin Runde Baru dake cikin karamar hukumar yola ta arewa da Al Amin Adamu Dan shekaru 25 mazaunin Samu naka dake cikin karamar hukumar yola ta kudu. Mutane biyun dai sun shiga komar Yan sandan ne biyo bayan fashi da sukayi wata mota da da fito daga Jalingo a tsakanin Mayo Belwa da Ngurore inda sukayi amfani da wuka suka soki direba a wuya wato Muhammed Sukeiman kana suka tafi da motar. Sai dai anyi rashin Sa a domin kuwa Yan sandan dake gudanar da sintiri akan hanyar sun Kai dauki cikin gaggawa inda motar tayi hatsari harma Daya daga cikin wadanda ake zargin ya rasa ransa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Kawo yanzu dai kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo M...