Hukumar yan sanda na rike da wani maishekaru 75 da kokarin yiwa yar shekaru 25 fyade a jahar Adamawa.
A yunkurinta na dakile aikata matsalar Fyade a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar tana tsare da wani mutum dan shekaru 75 da haifuwa bisa zarginsa da yunkurin yiwa wata yar shekaru 25 fyade a kauyen Mukuvinyi dake cikin karamar hukumar Hong a jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Ngurije ne ya baiyana haka a wata sanarwa da yarabawa manema labarai a yola. Wanda ake zargin mai suna Daniel Jaja yayi kokarin aikata fyaden ne biyo bayan gayyata da yayiwa yarinya zuwa gidansa, wanda kuma hakan yasa ya samu damar ganin zai aikata mata fyade, Bincike da aka gudanar ya baiyana cewa bai samu damar aikata fyadenba saboda yarinyar tayi amfani da reza wajen jimasa a gabansa, wanda hakan yasa yarinyar ta barshi da rauni wanda a yanzu hakama yana kauce a asibiti domin jinya. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola. yayi A...