Rundunan yan sandan jahar Filato ta dakatar da zirga zirgan mashuna a garuruwan Jos da Bukuru domin gudanar da bikin sabuwar shekara.
Rundunan yan sandan jahar Filato ta dakatar da zirga zirgan mashuna a cikin garin jos da Bukuru a wani mataki na inganta tsaro domin ganin an yi bukukiwar sabuwar shekara lafiya. Sanarwan hakan na kunshena a cikin wata sanarwa da kakakon rundunan yan sandan jahar filato DSP Alfred Alabo ya sanyawa hanu wanda aka rarrabawa manema labarai a Jos. A cikin sanarwan anjiyo kwamishinan yan sandan jahar Folato CP Bartholew N Onyeka ya bada umurnin dakatar da zirga zirgan maahunan wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen ganin anyi bukukuwar sabuwar shekara lafiya. Rundunan ta gargadi mazauna jahar da cewa har yanzufa dokan hana watsa tarsasin wuta dama buga ababe masu kara yananan nan daram saboda haka duk wanda aka kama da yiwa doka karan tsaye zai gamu da fushin hukuma. Kwamishinan ya tabbatarwa mazauna jahar cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin al umma fafin jahar baki daya. Ya kuma taya al ummar jahar kurnan bikin sabuwar shekara ta...